RAƊAƊIN TSADAR RAYUWA: Laƙanin Naira 8,000 ga marasa galihu cin fuska da raina talakawa ne – NLC

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC, ta bayyana cewa raba wa talakawa tallafin Naira 8,000 a mawuyacin halin da aka jefa ‘yan Najeriya a ciki, “cin fuska ne da raina masu wayau.”
Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a ranar Laraba, a cikin saƙon da ya aika wa ma’aikata, a Abuja, lokacin da ya ke jawabi a wurin zanga-zanga.
“Raba wa talakawa marasa galihu Naira 8,000 a wannan halin cin fuska ne a gare su, kuma an raina masu wayo. Mu na kira ga Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da muka yi da ita, wadda idan aka yi aiki da ita za ta zama alfanu ga talakawa a faɗin ƙasar nan.”
Bayan cire tallafin fetur, gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta fito da wasu tsare-tsaren sauƙaƙa ƙuncin rayuwa ga talakawan ƙasar nan da ma’aikatan gwamnati masu ƙaramin ƙarfi.
Sai dai kuma akasarin masu bayyana ra’ayin su na ganin cewa duk da tallafin ya yi kaɗan, to ba zai kai ga waɗanda su ka fi cancanta su ci moriyar sa ba.
Sannan kuma a sama da talakawa miliyan 100, za a bayar da tallafin ne ga mutum miliyan 12 kaɗai.
Sannan kuma wani bayani da Wale Edun ya yi a lokacin tantance shi minista, ya ƙara sa guyawun talakawa sun yi sanyi.
Edun cewa ya yi duk zafin talaucin mutum, ba za a ba shi tallafin na Naira 8,000 ba, sai ya na da asusun ajiyar kuɗaɗe a bankuna.
“Maganar tallafin nan duk shafa-labari-shuni ce. Har an shiga wata na uku kenan da cire tallafin fetur, amma ba a bayar da tallafin ko sisi ba. Babu wani ma’aikacin da ya samu tallafin Naira 1 tal daga gwamnati. Kuma har yanzu babu ma alamar motocin da aka ce za su samar da sassaucin kuɗaɗen zirga-zirgar ko guda ɗaya.” Haka Ajaero ya ja jaddada.
Ya ce kada Shugaba Tinubu ya shiga sahun shugabanni masu cika mutane da nuna damuwar su kan matsaloli kaɗai.
“Ya kamata Shugaban Ƙasa ya tashi tsaye ya sa a kamo manyan ɓarayin gwamnati da suka sace mana kuɗaɗe, su dawo da su.”
Haka shugaban na NLC ya bayyana a fusace.
Ya ce bayan wannan zanga-zangar, za su je su yi nazarin abin da zai biyo baya. Wannan inji shi zai bayar da ƙofar tafiya yajin aiki, idan gwamnati ba ta yi komai a kai ba.