Najeriya za ta karbi kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona miliyan 41 a karshen Satumba – Inji Shu’aib

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa Najeriya za ta karbi kwalaben ruwan maganin rigakafin cutar korona 41,282,770 a karshen watan Satumba 2021.

Shu;aibu ya ce maganin rigakafin na Oxford-AstraZeneca, Pfizer-Bio-N Tech/Moderna da Johnson & Johnson (J&J) na daga cikin miliyan 41 din da Najeriya za ta karba.

“Asusun COVAX ce za ta kawo Oxford-AstraZeneca da Pfizer-Bio-N na magani rigakafin sannan asusun da AU ta kafa ta kawo Johnson & Johnson (J&J).

“Mun samu tabbacin cewa asusun COVAX za ta kawo wa Najeriya kwalaben ruwan maganin rigakafin na Oxford/AstraZeneca/Moderna miliyan 3,924,000 a karshen watan Yuli zuwa farkon watan Agusta 2021.

“Asusun COVAX za ta Kara kawo kwalaben ruwan maganin rigakafin na Pfizer-Bio-N Tech/Moderna guda 3,930,910 a watan Agusta sannna asusun ta kara kawo wasu kwalabe ruwan maganin 3,577,860 na Pfizer-Bio-N Tech/Moderna.

” Sannan kuma asusun da AU ta kafa za ta kawo kwalabe ruwan magani 29,850,000 na Johnson & Johnson (Jassen) a karshen watan Satumba.

Allurar rigakafin korona a Najeriya

Idan ba a manta ba a ranar 5 ga Maris ne Najeriya ta fara yi wa mutane allurar rigakafin korona bayan ta karbi kwalaben maganin na AstraZeneca guda miliyan 4 daga wajen asusun COVAX.

Shu’aib ya ce zuwa yanzu gwamnati ta yi amfani da kashi 98% na kwalaben ruwan maganin rigakafin da ta karba wa mutum 3,938,945 a kasar nan.

Yi wa mutum allurar rigakafin korona da ruwan maganin AstraZeneca ya kunshi yin allurar sau biyu domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
Zuwa yanzu mutum 2,534,205 sun yi allurar rigakafin zango na farko sannan mutum 1,404,205 Sun yi allurar a zango na biyu.

Bayan haka Shu’aib ya ce hukumar ta samu rahoton cewa mutum 14,550 sun fuskanci matsaloli a jikinsu bayan da suka yi allurar rigakafin sannan mutum 148 sun yi fama da matsalolin da ya yi tsanani a jikinsu bayan yin allurar rigakafin.

“Sai dai har yanzu babu ran da aka rasa a dalilin yin allurar rigakafin.

Ya ce zuwa yanzu gwamnati ta dakatar da yi wa mutane allurar rigakafin zango na farko sannan tana shirin fara yi wa mutane rigakafin zango na biyu.

Shu’aib ya yi kira ga mutane musamman wadanda suka dara shekaru 17 da su hanzarta yin allurar rigakafin domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Sabuwan nau’in cutar korona ‘Delta’

Zuwa yan zu mutum 168,713 Suka kamu da korona a Najeriya inda a ciki an samu mutum daya dake dauke da sabuwan nau’in cutar ‘Delta’.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa nau’in cutar na ‘Delta’ ya fi saurin yaduwa.

Mutum 2,124 ne suka rasa rayukansu a dalilin kamuwa da korona a kasar nan.

Shu’aib ya ce maganin rigakafin korona na AstraZeneca na samar da kashi 88% na kariya daga kamuwa da nau’in ‘Delta’.

Ya yi kira ga mutanen da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar musamman yanzu da aka gano nau’in cutar Delta a kasan.

Binciken WHO ya nuna cewa nau’in ‘Delta’ ya yadu zuwa kasashe 104 a duniya.