INEC: Mutum 542,576 sun yi rajistan zabe ta hanyar CVR a yanar gizo

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa (INEC) Mahmood Yakubu ya bayyana cewa hukumar ta yi wa mutum 542,576 rajistan katin zabe ta hanyar (CRV) a yanar gizo a kasar nan.

Yakubu ya ce daga ciki mutum 456,909 sabin masu rajista ne, mutum 85,667 kuma wadanda suka nemi a canja musu wurin yin zabe ne.

Farfesa ya bayyana haka ne a Abuja ranar Talata a wajen zama da ya yi da shugabanin hukumar na jihohi 36 da Abuja.

An fara yin rajistan CVR ne ranar 28 ga Yuni 2021.

Yakubu ya ce daga cikin mutum 542,576 din da suka yi rajista mutum 356,777 matasa ne masu shekaru 18 zuwa 34, mutum 134,719 masu shekaru 35 zuwa 49, mutum 44,896 masu shekaru 50 zuwa 69 da tsoffi masu ‘yan shekara 70 zuwa sama su 6,184.

Ya ce akwai dalibai 156,446, masu sana’ar hannu 38,217, manoma da masunta 24,421, ‘yan kasuwa 150,145, ma’aikatan gwamnati 35,831 da mata masu aure da basu da aiki 8,334.

Akwai kuma mutum 129,182 da basu fadi irin sana’a ko aikin da suke yi ba.

Sannan kuma masu anyi wa nakasassu 6,558 rajistan.

Bayan haka Yakubu ya ce hukumar na sane da yadda ba kowa bane ke iya yin rajistan a yanar gizo amma kuma hukumar ka kokarin ganin an shawo kan matsalolin dake hana mutane yi domin kowa yayi, sannan kuma za ta bude sabbin wuraren yin rajistan 2,674 sannan ta zuba ma’aikata 5,346 a wadannan wurare.