A yanzu idan ka yabi Buhari cikin gungun jama’a, jifar ka za su yi – In ji tsohon Sanata

Wani tsohon sanata ya bayyana cewa saboda rashin zurfin tunanin sani irin ayyukan alherin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, a yanzu da mutum ya fito ya nuna jinjina ga irin ƙoƙarin Shugaba Buhari, jifar sa za a yi.

“Ba wani abu ne ya kawo haka ba sai matsalar ƙuncin rayuwar da mutane ke ciki. Amma maganar gaskiya Buhari ya yi ƙoƙarin da ya kamata a jinjina masa.”

Haka Sanata Andrew Uchendu, ya bayyana a wurin taron naɗa shi Uban Ƙungiyar Zaman Lafiya da Haɗin Kan Najeriya (Front for Peace and Unity).

“Idanun jama’a sun rufe an kasa ganin irin ƙoƙarin da gwamnatin Buhari ta yi. Yanzu ka shiga kasuwa ko dandazon jama’a a coci ka fara yabon Buhari, za ka ji irin hayagagar da za a riƙa yi maka. Wasu wuraren ma jifar ka kawai za a riƙa yi.”

Ya ce wannan gwamnatin ta yi rawar gani, “idan aka yi la’akari da yadda ƙasar nan ta ke tun daga 1992 har zuwa 2015, lokacin da Buhari ya karɓi mulki.”

“An bunƙasa noman shinkafa, an farfaɗo da man ja, an gyara tashoshin ruwa tare da gina wasu ƙananan tashoshin ruwan. An farfaɗo da tsarin jiragen ƙasa, kuma an gina gadoji.”

Uchendu ya ci gaba da bayyana nasarorin wannan gwamnatin, wadda ya ce rashin sani ne ke sa wasu ke ƙin ragwanta wa Buhari wajen caccakar sa.