MATSALAR TSARO: Gwamnatin Zamfara ta dawo da aikin ‘yan bangar kisan ‘yan bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana sanarwar dawo da aikin ‘yansakai, domin su taya jami’an tsaro ƙarasa murƙushe ‘yan bindiga a cikin dazukan jihar.

Shugaban Kwamitin Tsaro da Hukunta ‘Yan Bindiga na Jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ne ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da manema labarai.

Ya bayyana cewa a yanzu sojoji na samun gagarimar nasarar kakkaɓe ‘yan bindiga a jihar. Shi ya sa aka dawo da aikin ‘yansakai domin su ma su taimaka wajen zaƙulo ‘yan bindiga, wanzar da tsaro da kuma hana kai hare-hare a cikin al’umma.

Gwamna Bello Matawalle ne tun farkon hawan sa ya soke ayyukan ‘yan banga, inda ya zarge su da ruruta wutar kashe-kashe tsakanin Hausawa da Fulani.

“A wannan karo Gwamna Matawalle ya amince da dawo da aikin ‘yansakai, domin ƙara inganta tsaro, ganin yadda ake samun nasarar kakkaɓe su, a hare-haren buɗe masu wuta ta sama da sojojin sama ke ci gaba da yi.

“An dawo da ‘yansakai, amma an kafa wasu sharuɗɗa da ƙa’idojin gudanar da aikin na su. Kuma mu na sanar da cewa matakan rufe layukan waya da hana cin kasuwanni su na tasiri sosai.

“Hana cin kasuwanni ya rage satar shanu sosai, saboda babu kasuwar da ɓarayin shanu za su iya kaiwa su sayar.

“Shi ma rufe layukan wayoyin GSM ya na tasiri, domin babu masu bayar da rahoton halin da jami’an tsaro ke ciki ga ‘yan bindiga.”

Shinkafi ya nuna damuwar cewa Gwamnatin Jihar Zamfara na fama da ƙarancin kuɗaɗe. Saboda haka ƙofa a buɗe ta ke ga duk wani mai hali kuma mai niyyar bayar da taimako ko gudummawar sa, domin a ƙara samun ƙwarin guiwar kakkaɓe ‘yan bindigar da ke cikin dazukan Zamfara.

Dama kuma a ƙarshen makon jiya ne Gwamna Bello Matawalle ya ce babu sauran sasantawa da ‘yan bindiga, tsakanin mu da su sai kisa kawai.

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya bayyana cewa daga yanzu Gwamnatin Jihar Zamfara ba za ta sake nema ko yarda ta yi sulhu da ‘yan bindiga ba.

Ya ce saboda an sha yi masu wannan tayin a baya, kuma su na karya alƙawari da saɓa yarjejeniyar da aka yi da su.

Da ya ke magana a Gusau, Matawalle ya ce maimakon a yi sulhu da su, ya na kira ga jami’an tsaro su ci gaba da zaƙulo kamar ɓeraye a cikin daji, su na rafke su kawai.

“Gwamnati na ba za ta sake bai wa ‘yan bindiga afuwa ba, saboda an sha yi masu afuwa a baya, amma su na tayar da tubar su.”

Daga nan sai ya roƙi al’ummar jihar Jigawa su ƙara juriya da haƙuri tare da goyon bayan tsauraran matakan da jami’an tsaro ke ɗauka, su na zaƙulo ‘yan bindiga domin a dawo da dawwamammen zaman lafiya a yankin.

Matawalle ya ce luguden wutar da sojoji ke yi masu a yanzu, ya yi tsamarin da har ‘yan bindiga sun turo ‘yan aike, su na roƙon a yi sulhu tsakanin su da gwamnatin jiha.

Ya ce ‘yan aiken da ‘yan bindiga su ka tura masa sun shaida masa cewa sun tuba, sun daina garkuwa da kai hare-hare. Yanzu sulhu su ke nema su yi tsakanin su da gwamnati.

Ya ce a yanzu ‘yan bindiga masu yawan gaske sai arcewa su ke yi daga jihar Zamfara, sakamakon ruwan wutar da sojoji ke yi masu babu ƙaƙƙautawa.

Ya ce ‘yan siyasa su daina taimaka wa ‘yan bindiga ko ta wace hanya.

“Yan siyasa su ji tsoron Allah. Su daina sayen babura su na raba wa mutanen da ke sayarwa ga ‘yan bindiga su amfani da su wajen kai hare-hare.”

Matawalle ya ce Gwamnatin Jihar Zamfara za ta hukunta duk wani da aka samu ya na taimaka wa ‘yan bindiga, ko ya na sayen babura ana sayar masu.

Gwamnatin Jihar Zamfara dai ta kafa tsauraran dokokin taƙaita safarar kayan abinci, fetur da dabbobi da kuma dakatar da cin kasuwannin mako-mako, duk domin a samu sauƙin hana kai wa mahara kayan abinci da toshe masu hanyoyin samun makamai da kuɗaɗe.