BUHARI YA MURZA KAMBUN BASHI: Ya nemi amincewar Majalisar Dattawa ya ƙara kinkimo dala biliyan 4 da fam miliyan 710

A daidai lokacin da darajar kuɗin Najeriya ke ƙara taɓarɓarewar da har Dalar Amurka 1 ta kai Naira 550, a lokacin ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ke neman amincewar Majalisar Dattawa domin ya sake ciwo bashin dala biliyan 4 da kuma fam na Ingila 710.

Za a ciwo bashin ne daga wasu ƙasashe da manyan cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe da bankunan duniya, domin a cike giɓin kasafin kuɗin 2021.

Cikin wasiƙar da Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa, ya shaida masu cewa bashin tun a kakar kuɗaɗe ta 2018-2020 ya ke a cikin tsarin bashi.

Buhari ya ce za a yi amfani da tulin basussukan domin ayyukan raya ƙasa.

Ya ƙara da cewa za a tabbatar duk ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta amince za a yi har zuwa na amincewar cikin Yuni 2021, sun shiga cikin waɗanda za a aiwatar da kuɗaɗen basussukan.

Dala biliyan 4 dai a yanzu da Dala ke naira 550, daidai ku ke da Naira tiriliyan 2.2

Tulin Bashin Da Buhari Ke Ciwowa Ba Mai Kumbura Ciki Ba Ne -Gwamnatin Tarayya

Farkon watan Agusta ne Gwamnatin Tarayya ta ce tulin bashin da Najeriya ke ciwowa ba mai kumbura ciki ba ne.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa har yanzu bashin da Najeriya ke ciwowa bai kumbura mata cikin da zai iya fashewa ba.

Ministar ta ce har yanzu Najeriya ba ta tsallake ƙa’idar Gejin Tattalin Arzikin Cikin Gida na ba, inda ta ce har yanzu bashin bai wuce kashi 23 bisa 100 ba.

Zainab ta yi wannan bayani ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin.

Cikin watan shekaranjiya ne Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta bayyana malejin Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) ya ƙaru zuwa kashi 5.01 a watannin Afrilu, Mayu da Yuni na 2021.

Zainab ta ce ai babu wani abin damuwa, domin kuɗaɗen da ake rantowa ana yin ayyukan raya ƙasa ne da su, waɗanda su ka haɗa da aikin lantarki, titina, samar da ruwa da titinan jiragen ƙasa, waɗanda su ne ƙashin bayan inganta tattalin arziki.

“Mu na ciwo bashi a cikin yin taka-tsantsan ɗin da har yanzu ba mu wuce kashi 23 na Gejin Ma’aunin GDP ba.

“Na sha faɗa ba sau ɗaya ko sau biyu ba cewa babbar matsalar ƙasar nan ita ce ƙarancin kuɗaɗen shiga, waɗanda ƙarancin na su ke sa tilas a ke ciwo basussuka domin a yi ayyukan raya ƙasa da inganta tattalin arzikin cikin gida.”

Kwanan baya ne Majalisar Tarayya ta damu da tulin bashin da Gwamnatin Tarayya ke ciwowa, alhali hukumomi ba su zuba kuɗaɗen shiga asusun Gwamnanti.

Kwamitin Lura da Kuɗaɗen Gwamnantin Tarayya na Majalisar Tarayya ya nuna ɓacin rai ganin yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.62 domin narkawa a yi ayyukan raya ƙasa a kasafin 2021, amma kuma a gefe ɗaya hukumomin Gwamnantin Tarayya da yawa sun riƙe kuɗaɗen shiga sun ƙi zubawa a cikin Asusun Gwamnantin Tarayya domin a samu kuɗaɗen yin ayyuka.

Shugaban Kwamitin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya James Feleke ya ce, “a gaskiya ba mu jin daɗin yadda wasu hukumomin gwamnati ke riƙe kuɗaɗe ba su zubawa cikin asusun Gwamnanti, ita kuma gwamnati an bar ta fita gaganiyar ciwo basussukan da za ta yi ayyukan raya ƙasa.

“Don Allah ya zama wajibi mu tashi mu nuna kishin ƙasar mu don mu ci moriyar bunƙasar ta baki ɗayan mu.”

Feleke ya magana ne ganin yadda wasu hukumomin Gwamnantin Tarayya su ka kasa bada bayanai wasu kuma su ka ƙi zuba kuɗaɗen shigar su a Asusun Gwamnantin Tarayya tsawon lokaci.

Kwamitin dai na gayyatar Hukumomi ne ɗaya bayan ɗaya su na gabatar da bayanan kuɗaɗen shigar da su ke tarawa duk shekara, domin a ji yadda za a yi kirdadon kuɗaɗen shigar da za su tara daga shekarar 2022 zuwa 2024.