EL-CLASICO: Madrid ta luguiguita Barcelona, ta ɗirka mata kwallaye 3 a raga

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Spain ta luguiguita takwarar ta Barcelona da kwalleye uku a ragar ta.

Wasar wanda shine mafi girma da manyan kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar turai ke bugawa da aka yi masa lakabi da EL-CLASICO ya samu halarcin dubban ƴan kallo a filin Bernabau.

Benzama ya zura kwallo ta farko tun a farkon rabin lokaci, daga nan sai sai ɗan wasan Madrid, Valvade ya kara ta biyu duk kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Da aka dawo daga hutun rabin lokaci sai dan wasan Barcelona, Ferran Torres, ya rama kwallo ɗaya, daga nan kuma sai Madrid suka fusata, suka samu bugun daga kai sai mai tsaron gida. Rodrygo ya jefa kwallon cikin ragar Barcelona, kwallo ya zama dai uku a ragar Barcelona.

Wannan shine rashin nasara ta farko da Barcelona ta samu tun da aka fara buga wasan ƙwallon ƙafa na wannan kaka a kasar Spain.

Cikin haɗuwa 7 da Barcelona suka yi da Madrid, a baya-bayan nan, Madrid ta yi nasara a wasanni 6 kenan, Barcelona na da 1.

Wannan rashin nasara ya tada wa magoya bayan Barcelona hankali matuka, ganin irin siyayyan ƴan wasa da suka yi a bana.

Ga dukkan alamu dai kociyan Barcelona Xavi ba zai iya ba, domin ko a Champions League, akwai yiwuwar ba zai iya kai kungiyar zagayen gaba ba sannan kuma ya ruɗe, sai tangal tangal ya ke ba ya iya yin nasara idan ya haɗu da man yan kulub.