Magunguna 15 da ake yawan shan su ba bisa ka’ida ba da illolin yin haka

Jami’an lafiya musamman likitoci na yawan gargaɗi game da shan magunguna ba tare da izinin likita ko wani jami’in lafiya.

Dalilin da ya sa haka kuwa shine ganin irin illolin da ireiren waɗannan magunguna ke yi wa lafiyar mutane idan suka sha su batare da likita ya basu umarnin haka ba.

Domin guje wa matsaloli irin haka ya sa jami’an lafiya ke hana mutane siyan magunguna batare da takardar umani daga likita ba.

Bayan haka sakamakon binciken da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar ya sa ta gano wasu magunguna 15 da mutane ke yawan Shan su ba tare da izinin likita ba sannan da Lillian dake tattare da su Idan aka Yi amfani da su ba bisa ka’ida ba.

1. Diclofenac

Diclofenac magani ne da aka sarrafa domin kawar da ciwon jiki musamman masu fama da sanyi kashi wato ‘Rheumatism’ da turanci sannan da rage raɗaɗi Idan an samu karaya ko targade.

Da dama ana amfani da wannan magani domin kawar da ciwon Kai, kawar da laulayin haila na mata.

Yawan shan wannan magani ba bisa ka’ida ba na haddasa cututtuka kamar su gyambon ciki, lalata Koda da hantar mutum, haddasa bugawar zuciya da kawo shanyewar sashen kwakwalwar mutum.

2. Postinor

Postinor na daga cikin dabarun bada tazarar haihuwa da aka shigo da shi domin inganta lafiyar mata da yara kanana.

Jami’an asibiti sun ce mace za ta iya amfani da wannan magani domin kare ta daga daukan cikin da bata so na dan wani lokaci amma mafi yawan lokuta likitoci kan shawarci mata da su je asibiti domin a auna su domin gano dabaran da yafi dacewa da jikinsu yadda za su iya samun dabaran da zai dore fiye da postinor.

Sai dai mata da dama basu yin haka sun gwammace su rika amfani da wannan magani a matsayin dabara bada tazaran haihuwa mai dorewa.

Illolin Shan wannan magani ba bisa ka’ida ba sun hada da hana mace haihuwa, kawo cutar dake kama nono, yawan zubar wa mace gashin kanta, ciwon Kai, sa mace ta rika zubar da jini a lokacin al’adanta na wata-wata fiye da yadda ya kamata da birkicewar al’ada ga ƴa mace.

3. Felvin

Wannan magani ne da aka sarrafa domin rage ciwon jiki kamar su ciwon Kai da sauran su.

Mata da dama na amfani da wannan maganin domin rage musu laulayin al’adan da suke yi na wata-wata.

Illan yawan shan wannan magani sun hada da lalata Koda, hanta, haddasa cutar a‘Pancreas’ wato bangaren jikin mutum dake taimakawa wajen nika abinci.

4. Maganin tari (Cough Syrup)

Maganin tari na daga cikin magungunan da matasa ke yawan amfani da shi domin sa maye.

Wasu lokutan matasan kan Sha shi haka nan ko Kuma su gauraya shi da zobo ko Kuma lemun kwalba.

Illar shan wannan magani na saka maye, jirkicewar kwakwalwa da dai sauran su.

5. Ibuprofen

Shima maganin ciwon jiki ne da tsofaffin ke yawan amfani da shi musamman idan suna da matsala da kasusuwan su.

Ilolin shan wannan magani ba bisa ka’ida ba sun hada da sa mace yin bari, hawan jini, bugawqr zuciya, haddasa cutar asthma, kamuwa da cutar Koda da sauran su.

6. Shayin Coffee

Coffee shayi ne dake dauke da sinadarin ‘Caffeine’ wanda ke taimaka wa mutum wajen hana shi barci.

Ma’aikata, dalibai na daga cikin mutanen dake yawan Shan irin wannan shayi.

Illolin yawan shan coffee sun hada da hawan jini, hana mutum samun barci musamman a lokacin da ya kamata, ciwon kai, sa zuciyar mutum ya rika bugawa ba yadda ya kamata ba da kawo wa mace mai ciki matsaloli.

7. Tetracycline

Mutane musamman mata na yawan amfani da wannan magani domin kawar da cututtukan sanyi wasu Kuma su zubar da cikin da basa so.

Illolin wannan magani Idan aka sha shi ba bisa ka’ida ba sun hada da cutar da Koda, toshe kunnen mutum, lalata fatar mutum, illata kasusuwan jaririn dake cikin mahaifiyarsa.

8. Vitamin C

Vitamin C magani ne dake warkar da mura, rauni da inganta garkuwar jikin mutum.

Duk da haka Shan wannan magani ba bisa ka’ida ba na cutar da kodar mutum.

9. Paracetamol

Paracetamol magani ne da kowa ya Sani yana maganin ciwon Kai, zazzabi ko ciwon jiki.

Masu ta’ammali da muggan kwayoyi na amfani da wannan maganin sannan wasu matan ma na amfani da shi wajen dafa nama.

Illolin yawan shan wannan magani sun hada da cutar da hanta, Koda da sauran su.

10. Flagyl

Flagyl na daga cikin kwayoyin ‘Antibiotics’ da mutane ke yawan amfani da shi musamman idan mutum na gudawa.

Illolin yawan amfani da wannan magani ba tare da umarnin likita ba suna hada da hana maganin yin aikin da ya kamata ya yi a ‘ jikin mutum wanda suka hada wa warkar da rauni a jikin mutum, rashin jini a jiki, lalata kwakwalwa da jijiyoyi da sa mace mai karamin ciki bari.

11. Alabukun

Alabukin na daga cikin maganin da masu aikin ƙarfi ke sha domin su samu karfin ci gaba da aikon da suke Yi.

Masu ta’amali da muggan kwayoyi na yawan amfani da su domin ya sa su ji garau a jikinsu.

Bugawar zuciya, hawan jini, zuban jini ta cikin jikin mutum, lalata Koda da hanta na daga cikin illan dake tattare da Shan wannan magani ba bisa ka’ida ba.

12. Ampiclox

Ampiclox na daga cikin kwayoyin ‘Antibiotices’ din da mutane ke yawan amfani da shi ba tare da izinin likita ba.

Mata kan yi amfani da su wajen zubar da jaririn ciki, kawar da cutar sanyi.

Illolin Shan wannan magani ba bisa ka’ida ba sun hada da suma, cutar da naman jikin mutum da kamuwa da cututtukan dake kama Koda.

13. Cyproheptadine .

Wasu na amfani da wannan magani domin su kara kiba a jikinsu.

Maganin na haddasa cututtukan da suka hada da rashin jini a jiki, cutar da hanta, hana barci, birkita wa mace al’adan ta inda za ta rika ganin shi sau biyu a wata daya, rawan jiki da sauran su.

14. Lexothan

Ana amfani da wannan magani musamman idan mutum baya samun barci a lokacin da ya kamata.

Shan wannan magani ba bisa ka’ida ba na sa a riƙa samun da yawan sa mantuwa, kasala a jiki, rage wa namiji ko mace sha’awar yin jima’I, cutar da hanta da sauran su.

15. Tramadol

Tramadol na daga cikin muggan kwayoyin da hukumar NDLEA ke yaki da su musamman yadda maganin ke cutar da rayuwar matasa a kasar nan.

Shan wannan magani ba bisa ka’ida ba na sa ciwon Kai, hana mutum yin numfashi yadda ya kamata da yawan firgita haka kawai