TSUMAGIYAR KAN HANYA: An umarci ‘yan sandan Abuja su riƙa binciken motar ko wa kuma ko ɗan wa

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, mai lura da Shiyya ta 7, Kayode Egbetokun, ya bada umarnin jami’an sa su riƙa tsayar da motoci a Babban Birnin Tarayya Abuja ana yi masu binciken ƙwaƙwaf.
Egbetokun ya bayar da wannan umarnin a ranar Laraba, a lokacin da ya kai ziyara a Hedikwatar ‘Yan Sandan FCT Abuja.
Sai dai kuma ya yi gargaɗin cewa ahir ɗin su da ɓugewa su na karɓar na goro dagsma hannun masu motocin gida da kuma direbobin haya.
Ya ce su riƙa janyo hankalin mazauna cikin garuruwan gefen Abuja da sauran ƙauyukan domin a samu cikakken tsaro a cikin birnin tarayya da kuma sauran garuruwan da ke gefen sa.
Ya ce kuma su riƙa yin aiki tare da juna domin su kare wa aikin su martabar sa.
Ya ce duk wani laifi da ɗan Najeriya zai aikata, to za a ga ya danne haƙƙin wani ɗan ƙasa ne.
Ya ƙara da cewa antayo sabbin kuratan ‘yan sanda a cikin jama’a alama ce ta ƙoƙarin bunƙasawa da ƙarfafa aikin ɗan sanda a ƙasar nan.
Mataimakin Sufeton mai lura da Shiyyar Abuja ta 7, ya ce, “ku sani an haramta ‘yan jari bola a Abuja. Saboda haka a fatattake su, a hana su shiga Abuja.”
A ƙarshe ya ja kunnen su cewa a ƙarfafa bada hannu a danjojin fitilun kan titi.