GARKUWA DA FASINJOJIN JIRGIN ƘASA: Har yanzu ba a daƙile matsalar tsaro a Najeriya ba – Tinubu

Ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyyar APC, kuma babban jagoran ta, Bola Tinubu, ya ce garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa 31 da aka yi a Jihar Edo, ya tabbatar da cewa har yanzu ba a daƙile matsalar tsaro a ƙasar nan ba.
Tinubu ya yi wannan bayani a ciki wata takardar manema labarai da Kakakin Yaɗa Labaran sa, Tunde Rahman ya sa wa hannu kuma ya fitar a ranar Talata.
Jagaban dai shi ne ke ƙoƙarin ganin ya gaji kujerar mulki daga Shugaba Muhammadu Buhari.
A ranar Asabar ce wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da fasinjoji 31 masu jiran shiga jirgin ƙasa, daga garin Igueben a Jihar Edo zuwa Warri a Jihar Delta.
Wannan ne karo na biyu da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasa.
Na farkon shi ne na ranar 27 Ga Maris, 2022, wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.
APC wadda ke mulki tun da 2015 da 2019, ta yi alƙawarin idan ta kafa gwamnati, za ta magance rashawa, matsalar tsaro da inganta tattalin arziki.
Sai dai kuma Tinubu ya ce, “ganin yadda ‘yan bindiga su ka kwashe fasinjojin jiragin ƙasa su 31 a Jihar Edo, ya ce tabbas akwai sauran jan aiki matuƙa wajen kawar da matsalar tsaro a ƙasar nan.”