Kungiyar Direbobin mai ta janye yajin aikin da ta kira ƴaƴan ta su fara ranar Litinin

Kungiyar Direbobin tankunan mai ƙarƙashin ƙungiyar NUPENG ta janye yajin aikin da ta kira ƴaƴan kungiyar su fara daga gobe Litinin.
NTA ta ruwaito labarin janye aikin a tashar ranar Lahadi.
Dalilin da ya sa kungiyar Direbobi ta kira yajin aiki
Direbobin tankunan mai dake karkashin kungiyar Ma’aikatan Mai da iskar Gas ta Kasa sun shaida cewa daga ranar Litinin ba za su sake dauko mai zuwa wata jiha a kasar nan ba har sai an gyara hanyoyin kasar da suka lalace.
Shugaban kungiyar na reshen Kudu maso yamma Tayo Aboyeji ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai a Legas ranar Asabar cewa sun gaji da rasa direbobin manyan motocin mai a hanyoyin Najeriya.
” Ace wai idan mota daya ta yi lodi daga Legas sai ta yi kwana shida tana tafiya ba ta kai Abuja ba saboda tsananin lalacewar hanyoyin kasar nan. Bayan haka kuma ga hatsari da motocin mu ke yi duk saboda hanyoyin.
” Mun rasa direbobi da yawa a dalilin rashin kyan hanyoyin mu. Wannan shine dalilin da ya sa za mu fara yajin aiki daga ranar litinin domin yajin aiki ne yaren da gwamnati ta fi ganewa. Idan muka fara za su gyara hanyoyin. Kullum sai dai mu ji ana cewa gafara ga shanu amma ko kaho ba mu gani ba.
” Mun yi kukan, mun aika da takardu, mun bayyana musu kukan mu amma babu abinda gwamnati ta yi akan hanyoyin kasar nan. Ga ba daya duk sun lalace babu gyara. Ba mu taba ganin lalatacciyar gwamnati irin wannan ba. Saboda haka daga litinin babu dakon mai zuwa koina afadin kasar nan.
Aboyeji ya kara da cewa wannan karon ba za su daga wa gwamnati kafa ba sai an gyara hanyoyin Najeriya sannan za su dawo daukar mai a man yan motoci zuwa sassan kasar nan.