KASAFIN 2022: SERAP ta nemi Buhari ya rage Naira biliyan 26 da za a kashe a fadar sa

Kungiyar Rajin Kare Haƙƙin Jama’a ta SERAP ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya nuna halin dattako, ya zabtare kasafin Naira biliyan 26 da aka ware a kasafin shekara ta 2022 a Fadar Shugaban Ƙasa.

Za a kashe kuɗaɗen ne a asibitin da ke cikin fadar, tafiye-tafiye, kayan abinci da kayan shaye-shayen ruwa da lemuka da sauran ƙwalam da maƙulashe.

SERAP ta ce kuɗin sun yi matuƙar yawa, don haka kamata ya yi a rage domin a yi amfani da kuɗaɗen wajen inganta kiwon lafiya a faɗin ƙasar nan.

Haka nan kuma SERAP ta cika da mamaki ganin yadda Shugaban Ƙasa ke kukan rashin kuɗi, hsr ya ke neman ciwo bashi ɗin cike giɓin Naira tiriliyan 6, amma kuma shi ne zai kamfaci Naira biliyan 26 ya ce zai kashe ta a fadar sa.

A cikin wasiƙar wadda SERAP ta aika wa Buhari a ranar 9 Ga Okotoba, kuma Mataimakin Darakta Kolawole Oluwadare ya sa wa hannu, ya ce gaskiya a rage kuɗaɗen sun yi yawa.

Yayin da za a kashe Naira biliyan 24,835,805,231 wajen gina sabon asibiti a Fadar Shugaban Ƙasa, ciki har da kuɗin tafiye-tafiye da abinci da abin sha, a ciki za a danƙari abincin Naira miliyan 301,138,860 cikin shekara ɗaya.

Sai Naira miliyan 250,836,273 za a kashe wajen kayan shaye-shaye da abin da ya sauƙaƙa.