ALAWUS ƊIN NAIRA 75,000: Gwamnati za ta gindaya tsauraran sharuɗɗan bai wa ɗaliban jami’a masu karatu a fannin ilmin Koyarwa

Hukumar Rajistar Malaman Koyarwa ta Tarayya (TRCN), ta bayyana cewa za ta gindaya tsauraran sharuɗɗa wajen bai wa ɗaliban jami’a da na manyan kwalejoji wajen ba su alawus ɗin Naira 75,000 da aka sanar za a fara ba su.

Shugaban TRCN, Olusegun Ajiboye ne ya bayyana haka cewa za a riƙa bai wa ɗaliban jami’a masu kwas ɗin koyarwa Naira 75,000 a kowane zangon karatu.

Su kuma ɗaliban manyan kwalejojin ilmi za su riƙa kaɓar Naira 50,000 a kowane zangon karatu.

Ajiboye ya yi wannan ƙarin haske wurin lacca ranar Asabar domin zagayowar Ranar Malaman Koyarwa ta Duniya.

Ya ce duk da an fito da wannan tsari a lokacin da ake fama da ƙalubalen ƙarancin kuɗaɗen shiga, shirin ya na da muhimmanci matuƙa domin haka za a tsara shi tsaf kuma a fara biyan kuɗaɗen alawus ɗin ɗaliban cikin 2022.

Ya ƙara da cewa banda waɗannan kuɗaɗen ma akwai wasu alawus-alawus na tura malami yankunan karkara, kuma akwai kuɗaɗen kama haya ga malamai da aka tura koyarwa yankunan karkara.

Ajiboye ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Ilmi Adamu Adamu, waɗanda ya ce manyan ginshiƙsi ne na farfaɗo da martaba da ingancin ilmi a ƙasar nan.

Ya kuma yi magana a kan ƙarin wa’adin shekarun yin ritaya zuwa 65. Kuma shekarun aiki zuwa 40.