AMAI DA GUDAWA: Mutum 2,187 sun kamu cutar ta yi ajalin mutum 233 a cikin watanni 9 a Najeriya – NCDC

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta garggadi mutane da su kara mai da hankali wajen tsaftace muhallinsu tare da amfani da tsaftattacen ruwa domin dakile yaduwar cutar kwalara a kasar nan.

Hukumar ta yi wannan gargadi ne a dalilin yawan mutane da ka samu sun kamu da cutar a Najeriya. Mutum 2,187 suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 233 daga ranar 1 ga Janairu zuwa ranar 25 ga Satumbar 2022.

NCDC ta ce cutar zata ci gaba da yaduwa idan har mutane basu kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar da suka hada da tsaftace muhalli, amfani da ruwa mai tsafta da sauran su.

A rahotan da hukumar ta fitar daga ranar 1 ga Agusta zuwa 4 ga Satumba ya nuna cewa jihohin 13 na da kason kashi 92% na yaduwar cutar a shekarar 2022 a kasar nan.

Rahoton ya nuna cewa cutar ta fi yaduwa a jihohin Yobe, Borno and Taraba, Cross Rivers da Katsina.

Hukumar ta ce za ta hada hannu da kungiyoyin bada tallafi domin yakar cutar daga kasar nan.

Ga abubuwa 10 dake haddasa barkewar cutar a kasar nan

1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.

2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.

3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.

4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.

5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.

6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.

7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.

8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.

9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.

10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.