Kotu ta daure wani matashi mai ragargazar gwamna Matawalle a yanar gizo

Kotun Magistare dake Gusau a Jihar Zamfara ta aika da wani dan gwagwarmayar siyasa mai rubutu a Kafafen sadarwa na zamani, Mugira Yusuf, gidan gyaran hali a yau Juma’a saboda sukar gwamnan jihar Bello Matawalle da ya ke yi.

Shi dai Mugira na hannun damar tsohon gwamna Jihar Zamfara ne wato Abdul’aziz Yari kuma mai adawa da gwamna Bello Matatwalle a shafukansa na zamani ne.

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Zamfara ce ta kama Mugira Alhamis sannan ta gurfanar dashi gaban Kotun ranar Juma’ah bisa zargin da take masa na yada labaran karya da batanci da kuma zargin tada zaune tsaye.

Mai gabatarda kara, Ibrahim Aliyu ya fadawa Kotun cewa tun a ranar 17/01/2020 ne ma’aikatar tsaro da lamurran cikin gida ta Jihar Zamfara ne ta kawo wa rundunar ‘yan sanda Jihar korafin mai laifin watau Mugira tare da yi masa zargin tada zaune tsaye da kuma yada labaran karya da batanci.

Mai gabatar da karar yace wadannan laifukane da suka sabawa sashe na 114 dana 392 da kuma sashe na 393 na Dokoki.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta laifukan da aka zayyana ya aikata su.

Lauyoyin dake tsaya wa wanda ake kara, barrister Sirajo Garba Gusau da barrister A A Nahuce sun kalubalanci hurumin Kotun na sauraren Karar, cewa Kotun bata da hurumin sauraren Karar a matsayin wanda ake tuhuma musulmine saboda haka suna bukatar akai shi Kotun shari’ar Musulci kamar yadda Doka mai lamba 7 ta shekar 2002 ta tanada.

Sai Alkalin Kotun mai shara’a Sa’adu Gurbin Bore yace sai ranar Litinin ne Kotu zata yanke hukuncin kan bukatar lauyoyin dake tsaya wa wanda ake tuhuma ta bukatar da a maida Karar a Kotun shari’ar Musulci.

Sai dai kuma Alkalin Kotun ya saka ranar Litinin 25/10/2021 domin yanke hukunci dauke karar daga Kotun sa zuwa kotun sharo’ar kamar yadda aka bukata.