El-Rufai ya goyi bayan Majalisar Dattawa Tarayya domin kiran ‘yan bindiga da suna ‘yan ta’adda

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya bayyana goyon bayan sa ga Majalisar Tarayya, wadda ta yi kira ga Gwmnatin Tarayya cewa ta shaida wa duniya ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne kawai.

El-Rufai ya ce idan aka bayyana cewa ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne, to hakan zai ƙara zaburar da sojoji su darkake su a duk inda su ke, su na yi masu kisan kan-mai-uwa-da-wabi, ba tare da tsoron ƙorafe-ƙorafe daga bakunan ƙungiyi kare haƙƙi na kasashen duniya ba.

Gwamnan ya yi wannan furucin a ranar Laraba, a Kaduna, lokacin gabatar da Rahoton Matsalolin Tsaro Na Watanni Uku na kusa da ƙarshen shekara.

An gudanar da taron a Gidan Sa Kashim na Kaduna.

Ya na magana ne a kan ɓarnar da ‘yan bindiga ke ci gaba da yi a jihohin Arewa maso Kudu, ciki kuwa har da jihar Kaduna.

“Mu dama a jihar Kaduna mun daɗe da nuna goyon bayan a kira ‘yan bindiga da sunan ‘yan ta’adda kawai. Cikin shekarar 2017 mun rubuta wa Gwamnatin Tarayya wasiƙa mu ka nemi ta bayyana cewa ɗan bindiga fa ɗan ta’adda ne.

“Saboda sai fa an gwamnatin tarayya ya kira su da suna ‘yan ta’adda, sannan sojoji za su samu ƙarfin da za su riƙa yin shigar-kutse a cikin dazuka, su na yi masu kisan-kiyashi, yadda ƙungiyoyin ƙasashen waje ba za su riƙa yin matsin- lamba ga Sojojin Najeriya ba. Kuma ba za a ce Sojojin Najeriya sun karya dokar ƙasa-da-ƙasa ta ba.

“Don haka mu na goyon bayan matsayar da Majalisar Tarayya ta cimma, inda za mu ƙara aika wa Gwamnatin Tarayya cewa Jihar Kaduna na goyon bayan raɗa wa ‘yan bindiga sabon suna ‘yan ta’adda.

“Yin haka ne zai ba sojoji ƙarfin guiwar tashi tsaye haiƙan su murƙushe su, ba tare da wata tsugune-tashi ta biyo baya ba.”

El-Rufai ya nuna damuwa dangane da yadda a kullum ake samun rahotannin hare-haren ‘yan bindiga a jihar Kaduna, duk kuwa da irin maƙudan kuɗaɗen da jihar ke kashewa wajen samar da tsaro ga jami’an tsaro a jihar.

“Ina mai takaicin ganin yadda duk da ɗimbin kuɗaɗen da muke kashewa a ɓangaren tsaro, amma a ce har yanzu babu wata alamar raguwar hare-haren da ake kai wa jama’a a jihar.”

Daga nan sai ya roƙi gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 774,000, wato a ɗauki 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma, domin ayyukan inganta tsaro a Najeriya.