KORONA: An samu karin mutum 10 da suka mutu, 247 sun kamu a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa cutar korona ta yi ajalin mutum 10 sannan wasu mutum 247 sun kamu a jihohi 14 da Abuja ranar Alhamis.

Zuwa yanzu mutum 209,960 sun kamu sannan mutum 198,026 sun warke.

Mutum 9,084 na dauke da cutar sannan mutum 2,084 sun mutu.

Yaduwar cutar

Legas – 77,577, Abuja-23,001, Rivers-12,562, Kaduna-9,961, Filato-9,644, Oyo-8,732, Edo-6,519, Ogun-5,332, Kano-4,308, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,545, Kwara-3,930, Delta-3,514, Osun-2,818, Enugu-2,675, Nasarawa-2,462, Gombe-2,566, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-1,975, Imo-1,973, Bauchi-1,667, Ekiti-1,742, Benue-1,679, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,074, Bayelsa-1,125, Niger-1,056, Sokoto-796, Jigawa-587, Yobe-501, Cross-Rivers-625, Kebbi-458, Zamfara-276, da Kogi-5.

Bayan haka kasar Faransa ta bai wa Najeriya gudunmawar kwalaben ruwan maganin rigakafin cutar korona na AstraZeneca guda 501,600
Asusun COVAX ne ta yi jigilar magungunan zuwa Najeriya daga kasar Faransa sannan tuni har an adana su a wurin ajiyar maganin rigakafin da gwamnati tarayya ta samar a tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce wannan gudunmawar ya nuna goyan baya da kasar Faransa ke yi kan yaki da cutar da Najeriya ke yi.

Shu’aib ya tabbatar cewa gwamnati ta samar da ingantattun wuraren ajiyar maganin rigakafin cutar.

Shu’aib ya kara da cewa gwamnati ta tsara hanyoyi da za su taimaka wajen tabbatar da an yi wa mutane allurar rigakafin da magungunan a duk jihohin dake kasar nan.