Kotu ta bada belin barawon babura 100 kan naira miliyan 1

A kotun majistare dake Akure jihar Ondo ne ranar Talata aka gurfanar da Wasiku Okunola da kama shi da laifin sace babura 100 a karamar hukumar Akure.
Lauyan da ya shigar da karar Olusegun Akeredolu ya ce Okunola ya sace baburan tare da taimakon wani Bola da ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo.
Ya ce Okunola ya saci wadannan babura tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023.
Akeredolu ya ce jami’an ‘yan sanda da DSS sun dauki tsawon watanni har uku suna farautar Okunola kafin suka kama shi.
Ya roki kotun da ta daga shari’ar domin fannin da ta shigar da karar ta samu lokacin neman shaidun da za ta gabatar a gaban kotun.
Akeredolu ya kuma roki kotun kada ta bada belin Okunola amma ta daure shi saboda yana iya arcewa.
Sai dai lauyan dake kare Okunola ya musanta haka yana mai cewa laifin da Okunola ya aikata ya cancanci a bashi beli sannan ya tabbatar cewa Okunola ba zai gudu ba.
Alkalin kotun Damilola Sekoni ya bada belin Okunola akan Naira miliyan daya tare da gabatar da shaidu biyu dake aiki.
Sekoni ya ce kowannen su da Okunola zai gabatar a kotun zai kawo Naira miliyan daya ya ajiye a kotu da idan Okunola ya gudu kotu za ta rike wadannan kudaden da suka ajiye a hannunta.
Ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 24 ga Maris.