KASHE-KASHEN JAJIBIRIN ZAƁEN GWAMNONI: An kashe mutum uku a harin da ‘yan daba su ka tarwatsa taron APC a Oyo

Wani gungun ‘yan daba ɗauke da muggan makamai sun kutsa zauren taron magoya bayan APC a Ile-Tintun da ke ciki Ƙaramar Ibadan ta Kudu maso Gabas, inda rahotanni su ka haƙƙaƙe cewa sun bindige mutum uku har lahira.
A harin wanda aka kai ranar Alhamis, kwanaki biyu kafin zaɓen gwamnoni, sun kuma lalata kayayyaki masu yawa mallakar magoya bayan APC. Sannan kuma an tabbatar da cewa wasu da dama sun ji raunuka ya yamutsin.
Ɗan takarar APC a majalisar dokokin Oyo da ke Mazaɓa ta 2, mai suna Wariths Alawuje, ya ce lokacin da aka kai mummunan harin ya na cikin mahalarta taron, amma dai ya tsira da kyar, ba a harbe shi ba.
Ya ce: “Mu na tsakiyar tattauna batutuwa da shugabannin jam’iyya, sai mu ka ji ‘yan wata jam’iyya sun tunkaro inda mu ke a cikin ofishin mu.
Mutanen mu sun jira su tafi, amma ba a daɗe ba, sai mu ka ga wani jigo a jam’iyyar su ya na raɗa wa wani magana. Daga nan sai mu ka fara jin ƙarar harbe-harben bindigogi. An lalata mana dukiyoyi, motoci, gidaje da ke maƙautaka da ofishin. Kuma sun kashe wasu daga mahalarta taron.”
Wani ɗan APC mai suna Adewale, ya shaida wa Premium Times cewa maharan sun riƙa fiddo bindigogi kamar za su tashi garin daga wanzuwa.
“Hari ne kawai na ɗibgaggun ‘yan siyasa ne. Saboda lokacin da su ka shigo mana, su na yi ne kamar wadanda aka turo su kashe mu.
“Ya zama dole ‘yan sanda da sojoji su tashi tsaye sosai a wuraren zaɓen gwamnoni.”
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Oyo, Adewale Osefeso dai har zuwa lokacin haɗa wannan labarin, bai amsa kiran da wakilin mu ya yi masa ba.