ZAƁEN GWAMNONI YA ƊAU ZAFI: Faɗa ya ɓarke lokacin da ‘yan-ta-kife su ka kutsa ofishin INEC, su ka ragargaza akwatin zaɓe

Rikici ya ɓarke yayin da wasu ‘yan-ta-kife su ka danna cikin ofishin Hukumar Zaɓe, su ka lalata akwatin zaɓe.
‘Yan sandan da aka tura sun yi tsaye cirko-cirko su na kallon faɗa, maimakon su shiga su hana, ko su bada baki a daina.
Rikicin ya ɓarke tun ƙarfe 7:48 na safiya, a Ranar Zaɓe, a Cibiyar Rajistar INEC da ke Mbiaso Ward 4, cikin Ƙaramar Hukumar Nsit Ibom cikin Jihar Akwa Ibom.
Wani mutum ne musabbabin rikicin, ya yi kukan kura ya fizgi akwati daga hannun wani jami’in zaɓe, kuma ya kwantsama shi ƙasa, ya ragargaje.
Wani ma’aikacin gwamnati da ya ɗauki bidiyon rikicin ya kusa shan dukan tsiya, yayin da magoya bayan sauran jam’iyyu su ka yi barazanar canja masa kamanni.
Wanda ya ragargaje akwatin dai ɗan PDP ne, ya shiga ofishin a lokacin da ake ƙoƙarin tantance kayan zaɓe.
A wani labarin kuma, an yi garkuwa da ɗan takarar mataimakin gwamna kan hanyar zuwa jefa ƙuri’a.
An yi garkuwa da ɗan takarar mataimakin gwamnan Jihar Cross River na jam’iyyar YPP, Agbor Onyi.
Tuni dai Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta Cross River su ka tabbatar cewa an yi garkuwa da shi ne da wasu mutum uku, waɗanda cikin su har da Mataimakin Sufurtandan Imagireshin.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sanda na jihar, Irene Ugbo ta shaida wa manema labarai cewa an sace su a ranar Alhamis, kan hanyar Kalaba zuwa Ogoja.
Ta bayyana sunan jami’in Imagireshin da Imojara Imojara.
Ta ce an yi garkuwa da su huɗun ne yayin da su ke kan hanyar tafiya garin su domin yin zaɓe.
“Waɗanda tsautsayin ya ritsa da su, su na kan hanyar tafiya ce a cikin motar ƙirar Toyota Corolla, lokacin da masu garkuwa su ka tare su, kuma su ka yi cikin daji da su.
“Ɗaya daga cikin waɗanda ke cikin motar matar wani hadimin Gwamna Ben Ayade ce”. Inji Kakakin ‘Yan Sanda.
Yan sanda sun ce su na bakin ƙoƙarin gano su kuma su ceto su.
Majiya ta bayyana cewa masu garkuwa sun nemi a biya su Naira miliyan 60, amma daga baya su ka rage zuwa Naira miliyan 40.
Tuni dai a wasu rumfunan zaɓe aka fara kaɗa ƙuri’u a jihohi daban-daban.