KORONA: Kasar Kanada ta baiwa Najeriya tallafin dala miliyan 9.2, domin ci gaba da yin rigakafin Korona

A ranar Laraba ce Gwamantin Tarayya ta
amshi tallafin dala 9,261,920, domin hanzarta ayyukan rigakafi na cutar korona.

Babban Jakadan Kanada Mista Christoff, ya ce tallafin ya ce alama ce ta ƙarfafa alaƙar ta da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, domin tallafa wa Najeriya.

Christoff ya ce a yanzu ba a cewa cutar korona babbar barazana ce a duniya, to amma akwai buƙatar bunƙasa tsare-tsaren kiwon lafiya.

“Ya zama wajibi a riƙa yi wa jama’a rigakafi da kuma wasu tsare-tsaren kula da lafiya.”

“Saboda har yanzu akwai rahotannin cutar a duniya cikin ƙasashe daban-daban.

“Kuma zan sake jawo hankalin waɗanda suka kammala riga-kafi cewa su ci gaba da kare lafiyar su, ta hanyar matakan kariya.”

Da ya ke magana, Shugaban Hukumar NPHCDA, Faisal Sha’ib, ya ce an samu galabar yi wa kashi 75% rigakafin farko.

Ya ce a yanzu za a bada karfi a Ribas, Delta, Legas, Ebonyi,
Akwa-lbom, Bayelsa, Katsina, Taraba, Edo, Anambra da wasu wuraren.