Tun da aka kara kudin mai mutane suka daina kawo motoci gyara, aljihun sun bushe – Makanikan Bauchi

Makanikan motoci a jihar Bauchi sun koka da yadda masu motoci suka daina kawo motocin su gyara, tun bayan da a cire tallafin.
Makanikan sun ce wannan matsala ya fara ci musu tuwo a kwarya domin komai na neman ya tsaya cak, saboda matsalar tsadar mai da ake fama dashi.
Malam Abati Usman, ya ce yawan motocin da yake aiki a kai kusan kullum sun ragu matuka. Tsadar mai ya sa mutane duk sun ajiye motocin su a gida, ko sabis ba su zuwa yi. Mu kuma nan aljihu ya bushe.
Wani makaniken Marsandi ya ce abin fa ya yi matukar muni, ba a kawo gyaran motoci yanzu. Wasun mu ma sun fara hakura da aikin makanikancin kawai, kuma duk saboda wahalar mai ne.
Wadanda suke koyon aiki ma sun daina zuwa aikin, saboda tsadar kudin mota, wadanda suke kusa ne suke kokarin garzayowa.
Shima Timothy Audu, ya ce a baya su kan yi aikin motoci akalla 10 zuwa 13, amma yanzu da kyar mota daya ke shigowa gyara.
Makanikan sun ce ” Yanzu dai tsakani da Allah, dole mu fara neman wata sana’ar domin kaninkance na neman ya gagare mu. Ba akawo motoci gyara, kunga kawai matsala kenan.