Rajistar sunayen masu karɓar tallafi ta ƙasa ba sahihiya ba ce – Gwamnoni

Majalisar Tsara Tattalin Arziki ta Ƙasa, ta ce Gwamnoni su fito da tsarin cikakkar rajistar marasa galihu, domin wadda Gwamnantin Tarayya ke amfani da ita ba sahihiya ba ce.
Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo ya yi wannan bayani, bayan tashi daga taron su a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Alhamis.
Ya ce ya dace tallafin da za a fara rabawa ya kasance yana isa ga marasa galihu.
“Ya kamata mu faɗa wa kan mu gaskiya cewa babu wata sahihiyar rajistar marasa galihu a faɗin ƙasar nan.”
Ya kuma yi bayani cewa Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni su fito da tsarin turawa marasa galihu alawus-alawus na rage tsadar rayuwa, gwargwadon karfin su.”
“Misali Gwamnonin da ba su biya kuɗaɗen fansho ba, su yi azamar biya. Waɗanda ba su biya ariyas ba, to su fara amfani da kuɗaɗen tallafin su bayar.
“Gwamnoni su ma tilas su rage almubazzaranci, domin a halin yanzu babu wani dalilin da gwamna zai fita da tawagar motoci 20.
“Ya kamata a cikin wannan halin a yi abin da ke daidai da talaka.”