Kanawa sun yi ragaraga da NECO cikin Ɗalibai 89,000 da suka rubuta jarabawar, ɗalibai 80,000 sun cinye duka darussa 9 – Kwamishina Kiru

Kwamishina Ilmin Jihar Kano Sanusi Kiru ya bayyana cewa ɗalibai da suka rubuta jarabawar NECO a shekarar 2021 duk sun cinye darussa 9 da suka rubuta.

Kiru ya faɗi haka ne kamar yadda Daily Nigerian ta buga a lokacin da yake bayanin nasarorin da ma’aikatar sa ta samu a shekarar 2021 a bainar manema labarai a Kano.

” Mun fi duka jihohin kasarnan yawan ɗaliban da suke rubuta jarabawar kammala sakandare.

” A cikin shekarar 2021, ɗaliban mu 89,000 suka rubuta jarabawar kammala sakandare, ciki kuwa 80,000 duk sun samu Kiredit a darussa 9 duka. Wannan babban nasara ce da aka samu.

Kiru ya kara da cewa hakan nuni ne cewa ilimi ya na samun muhimmiyar kula karkashin wannan gwamnati. Sannan kuma ya ce gwamnati ta kashe akalla naira miliyan 500 wajen biyan ƙudin jarabawar ɗalibai haɗi da waɗanda masu hali kan biya wa ɗalibai.