Gwamnatin Kaduna ta maida tsarin karatun makarantun jihar zuwa kwanaki 4 duk Mako

Kwamishinan Ilimin jihar Kaduna ta sanar da buɗe duka makarantun jihar ranar 10 ga watan Janairu bayan hutun makonni uku da aka yi na karshen shekara.

Bayanin haka na ƙunshe ne a wata takarda da ma’aikatar ilimin jihar karkashin kwamishina Halima Lawal ta rabawa manema labarai a garin Kaduna ranar Lahadi.

Gwamnati ta umarci makarantun jihar kaf dinsu su maida tsarin Karatu zuwa kwanaki huɗu duk mako daga wannan zango na karatu da aka dawo.

Idan ba manta ba gwamnatin jihar Kaduna ta rage ranakun aiki a ma’aikatun jihar zuwa Kwanaki 4 tun a watan Disamba.

A sanarwar wanda mai ba gwamnan jihar Nasir El-Rufai shawara kan Yaɗa labarai Muyiwa Adekeye ya fitar ya ce gwamnati ta yi haka ne don ma’aikata su rika samun daman zama da iyalansu na dan wani tsawon lokaci su taya matan su dawainiyar gida.

Kwamishina Halima tace ɗalibai a jihar Kaduna za su koma makaranta ranar Litinin 10 ga wata sannan makarantun kwana za su amshi dalibai tun daga ranar Lahadi 9 ga wata.

” Bayan haka gwamnati na kira ga makarantun jihar da su tsaurara matakan tsaro a makarantun su sannan su gaggauta sanar da jami’an tsaro idan aka samu matsalar tsaro a makarantu.

” Sannan kuma ka’idojin Korona na nan daram. Kowacce makaranta dole ta kiyaye waɗannan dokoki.

A karshe kwamishina Halima ta bayyana wasu lambobi kamar haka wanda za a kira jami’an tsaro odan buƙatar haka ya taso – 09034000060 ko 08170189999.