DAJIN DAKE KAMA MAHAIFA: WHO ta yi kira a tsananta yin rigakafi

Idan ba a manta ba sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar a shekarar da ta gabata ya nuna cewa akalla mata 311,000 ne ke rasa rayukan su a duniya a dalilin kamuwa da cutar dajin dake kama al’aurar mace.

Mace kan kamu da cutar dajin dake kama al’aurar ne a dalilin tsalle-tsalle da mata kan yi daga wancan namijin zuwa wancan.

A dalilin haka shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen duniya da su hada karfi da karfe wajen ganin sun yi wa mata allurar rigakafin cutar domin kare su daga kamuwa da ita.

Ghebreyesus ya ce sauran matakan da ya kamata a dauka wajen samar wa mata kariya daga kamuwa da cutar sun hada da wayar da kan mutane game da cutar, yi wa mata masu shekaru 35 da 45 gwajin cutar da samar da ingantaccen kula ga mutanen da suka kamu da cutar.

Ghebreyesus ya ce yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar nan da shekaran 2030.

A Najeriya masu fama da cutar daji na shiga cikin mayuyacin hali a dalilin rashin samun kula da tsadar maganin cutar.

Atajirai da dama a Najeriya na fita zuwa kasashen waje domin samun ingantacen kula a duk lokacin da suka kamu da cutar.

Domin guje wa irin haka wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin ganin an fara yi wa mutane gwajin cutar tare da saman kula a kasar nan.

A shekaran 2019 ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa gwamnati za ta bude asusu domin tallafa wa masu fama da cutar daji a kasar nan.

Sai dai masu fama da cutar sun ce har yanzu basu fara samun tallafi daga gwamnati ba.

Shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar tarayya, Tanko Sununu ya ce har yanzu gwamnati na kokarin tsaro matakan da za su taimaka mata wajen bude asusun da yadda za ta raba wa asibitoci kudaden da aka tara domin tallafawa masu fama da cutar.