Hukumar kwastam ta kama haramtattun kaya na naira miliyan 112 a Fatakwal

Hukumar kwastam dake kula da shiyar Area 1 a Fatakwal ta kama haramtattun kaya da kudinsu ya kai naira miliyan 112.
Shugaban hukumar Ibrahim Muhammad ya sanar da haka a garin Fatakwal a farkon wannan mako.
Ibrahim ya ce hukumar ta kama wadannan kaya a cikin kwantena hudu inda a ciki akwai galan 2,965 na man gyada ne da gwamnati ta hana shigowa da su kasar nan.
“Hukumar ta kama wadannan kaya bayanan samun bayanan sirri da ta samu da bincike ya nuna cewa an boye man gyadan a cikin tiles din da ake ado da shi a daki da kayan wutan lantarki.
“Hukumar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu wajen shigo da wadannan kaya.
Bayan haka Ibrahim ya ce hukumar ta kama dilar gwanjo 481, adduna 700 da cebur 107.
Bayan haka Ibrahim ya ce hukumar ta tara sama da Naira biliyan 92.32 a shekarar 2022 inda a shekarar 2021 ta tara naira biliyan 81.32
Ya ce a shekarar da ta gabata hukumar ta samu Karin kashi 12% na kudaden shiga.
Ibrahim ya ce hukumar ta samu Kari a kudaden shiga saboda harajin da rake kwasa daga kamfanonin giya da kuma tashoshin ruwa na Kasa.