Cutar DIPHTHERIA ta yi ajalin mutum 25 a jihar Kano

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa cutar ‘Diphtheria’ ta yi ajalin mutum 25 a jihar Kano.

NCDC ta bayyana cewa ta dauki matakai domin dakile yaduwar cutar da ta bullo a jihohin Legas, Osun, Yobe sannan ya zu da jihar Kano.

Hukumar ta ce zuwa yanzu ba ta da masaniyar yawan mutanen da suka kamu da cutar da yawan da cutar ta kashe a kasar nan sai sai kwamishinan lafiyar jihar Kano Aminu Tsanyawa ya tabbatar cewa cutar ta yi ajalin mutum 25 a jihar.

Hukumar ta ce ta hada hannu da ma’aikatun lafiya na jihohin da cutar ta bullo domin dakile yaduwar cutar.

Cutar Diphtheria

Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa ta.

Cutar ya fi kama yara da manya musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cututtuka da ake Yi wa yara ba.

Cutar kan kama makogwaro, hanci sannan wasu lokuta fatar mutum.

Cutar ya fi yaduwa idan ana yawan zama kusa da wadanda suke dauke da ita, idan mai dauke da cutar ya rika yin tari ko atishwa a tsakanin mutane.

Alamun cutar sun hada zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogwaro, idanu su yi jajawur, tari da Kumburin wuya.

Wasu lokuta mai fama da cutar zai rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa a kusa da makogwaro wanda ke hana mutum iya yin numfashi.