Kodinatan Kwankwaso na NNPP a jihar Bauchi ya watsar da tafiyar, ya koma PDP

Babayo Liman kodinatan dan takarar Shugaban kasa na jami’yyar NNPP Rabi’u Ƙwankwaso na jihar Bauchi ya yi watsi da tafiyar ya koma jami’yyar PDP.
Liman wanda shine sakataren jam’iyyar na shiyar Arewa maso Gabas ya sanar da haka ranar Litini a taron da ya yi da namema labarai a garin Bauchi.
“Ina so na sanar wa mutane duka musamman ‘yan jami’yyar NNPP na shiyar Arewa maso Gabas, jihar Bauchi da Najeriya duka cewa na fice daga jami’yyar NNPP na koma jami’yyar PDP.
“Na Kuma sauka daga kujerar kodinatan kamfen din Rabi’u Ƙwankwaso da matsayina na sakataren jami’yyar na shiyar Arewa maso Gabas.
“Daga yau ina so na sanar wa mutane cewa na fice daga jami’yyar NNPP na koma jami’yyar PDP.
Liman ya ce ya fice daga jami’yyar NNPP da magoya bayan da saboda jami’yyar bata da tsarin da zai sa ta yi nasara a zaben da ka tunkara.
Ya ce ya kuma yanke hukuncin canja sheka saboda matsalolin rashin hadin kai da ake fama da shi a jami’iyyar rashin adalci a shugabancin jam’iyyar.
A dalilin haka ya sa yake kira ga mutane da su zabi ‘yan takaran jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Shugaban jami’yyar PDP na mazabar Sarkin-Baki a jihar Bauchi Yusuf Marafa ya yi wa sabbin shiga jami’yyar maraba sannan ya tabbatar musu cewa jam’iyyar PDP jami’yyar ce dake da hadin kai kuma na kowa da kowa ne