Gwamnonin Kasar nan ne matsalar Najeriya ba Buhari ba – Na’abba

Tsohon kakakin majalisar Tarayya, Ghali Na’abba ya zargi gwamnonin kasar nan cewa sune matsalar Najeriya.

Ghali ya ce da gwamnoni na yin aiki a matsayin su na shugabanni musamman a shugabancin jam’iyyun da wasu matsalolin ba su kai yadda suke ba a yanzu.

” Gwamnoni sun zama sune wuka sune nama a jam’iyyun kasar nan. Babu wanda ya isa a kan su sai yadda suka so ake yi.

Na’abba ya ce tun farko an baiwa gwamnonin jihohin kasar nan karfin da bai kamata a basu ba.

Hakan yasa sai yadda suka so suke yi.

” Na yi takara sau biyu ban taba biyan wasu kudi ba kafin suka zabe. Amma wai na fito neman sanata a Kano, sai aka ce min wai sai na ba wasu kudi kafin a zabe ni, dalilin da ya sa kenan na hakura na janye.

Na’abba ya ce suna shirin kafa sabuwar jam’iyya a kasar nan wadda nan ba da dadewa ba za su bayyana ta, ya kuma kara da cewa burin sa na zama Sanata na nan.

Idan ba a manta ba, Na’abba na cikin wadanda suka rika taka wa Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo birki a lokacin yana kakakin majalisar Wakilai wajen kalubalantar wasu manufofin gwamnatin sa da dama a wancan lokacin.

Sai dai kuma hakan yasa da karfin tsiya Ghali ya rasa kujerarsa na zama dan majalisa.

Bayan haka ya koma jam’iyyar APC amma bai dade ba, ya fice daga jam’iyyar ya hakura gaba daya ya hakura da kowacce jam’iyya.