SATAR ƊALIBAI A SAKANDAREN TARAYYA TA KEBBI: Ƴan bindiga na neman hana yara karatun boko a Arewa

Ƴan bindiga su sake darkakar ɗaya daga cikin makarantun sakandare su ka kwashi ɗaliban da ba a bayyana adadin su ba a jihar Kebbi.
A wannan karo sun dira Kwalejin Gwamnatin Tarayya, ta garin Yauri su ka kwashi ɗalibai da malaman makaranta.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an kwashi ɗaliban amma ba ta bayyana adadin su ba.
Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar ya shaida a wata sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda masu gadin makarantar sun yi artabu da maharan har aka harbe jami’i ɗaya.
Ya ce a kan babura su ka darkaki Yauri, amma daga cikin dajin Rijau na Jihar Neja su ka fito, kuma a can su ka nausa da ɗaliban da su ka kwashe.
Rahotanni a wasu kafafen yaɗa labarai sun tabbatar da cewa duk da cewa ‘yan bindigar a babura su ka kai harin, sun kwashi wasu ɗaliban a cikin mota.
‘Yan sanda sun tabbatar wa iyayen yaran da cewa su ka cikin daji su ka farautar ‘yan bindigar.
Satar Ɗalibai: Yadda Karatun Boko Ke Neman Gagarar ‘Ya’yan Talakawa:
Kamar yadda Boko Haram su ka riƙa sace ɗaruruwan ɗalibai a baya, su ka ‘yan bindiga sun bi sawun su wajen yawan kwasar ɗalibai ana yin garkuwa da su.
A cikin 2021 an kai farmaki a makarantun sakandare da su ka haɗa da Jihar Katsina da aka kwashi ɗaruruwan ɗalibai a Ƙanƙara, sai Jihar Zamfara da Jihar Neja inda aka kwashi ɗalibai a garuruwa uku. A Katsina ma an saci ɗaliban Islamiyya 400 kan hanyar komawar su gida tsakar dare daga taron Maulidi.
A lokacin da aka kwashi ɗalibai na baya bayan nan a Kebbi, wasu ‘yan bindiga na riƙe da ɗaliban Islamiyya 139 na Tegina a Jihar Neja.
Sannan jihar Kaduna ta sha fama ita ma da kwashe ɗalibai tun daga na jami’a har zuwa na babbar kwaleji.
Sannan idan ba a manta ba dai a cikin wannan shekarar ‘yan bindiga sun kai samame a Kwalejin Turkish Collage da ke Kaduna, amma sojoji su ka fatsttake su.
Yanzu haka akwai wasu ɗaliban Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke hannun ‘yan bindiga. Kuma makarantar da ke Zariya ta kasance a rufe.
Yayin da ba a san adadin yawan ɗaliban Yauri da aka kwashe ba, haka nan kuma ba a san ranar da za a sako su ba. Duk kuwa ya yawan alwashin da jami’an tsaro ke sha cewa su na farautar maharan.