Bawan EFCC zai fara rangadin dukan kantama-kantaman rukunin gidajen da aka gina ko aka saya da kuɗaɗen sata

Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa, ya bayyana cewa hukumar ta bankaɗo yadda ake ta ginawa da kuma sayen kantama-kantaman rukunin gidaje da katafaren plaza-plaza da kuɗaɗen da aka sata na talakawa daga aljihun gwamnatin tarayya.

Ya ce a yanzu an wayi gari a Abuja, Lagos da Fatakwal sai rige-rige da haukan gina rukunin gidaje da manyan plaza-plaza ake ta yi.

“Irin yadda ake ta narka maƙudan kuɗaɗe wajen gina maka-makan plaza-plaza da rukunin gidaje barkatai a Abuja, Lagos da Fatakwal abin damuwa matuƙa. Don haka tilas mu bi su ɗaya-bayan-ɗaya mu tantance wadanda aka gina ko aka saya da kuɗaɗen sata, domin mu ƙwace.”

A kan haka ne Bawa ya bayyana cewa ya na buƙatar haɗin kai da goyon bayan kafafen yaɗa labarai domin samun gagarimar nasarar aikin da shi da hukumar sa su ka ɗauko haramar farawa.

Shugaban EFCC ya yi wanann bayani a ganawar da ya yi da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, a ranar Alhamis.

“Abin mamaki a kullum kuɗin manyan gine-gine sai tashi farashin su ke yi. Kuma a kullum sai ƙara narka biliyoyin kuɗaɗe ake yi ana ginawa kuma ana sayen maka-makan gine-gine. Sai ka rasa daga inda kuɗaɗen ke fitowa.”

Bawa ya buga misali da yadda aka sayi wasu kadarorina dala miliyan 3.7 da kuma yadda wani Kola Aluko ya sayi danƙareren dogon ginin AVIC TOWERS a Lagos, kan kuɗi dala miliyan 55.

Lamarin Akwai Harƙalla A Ciki:

Bawa ya ƙara da cewa sun gano akwai yiwuwar bambancin ainihin haƙiƙanin farashin kadarorin da kuma farashin da aka saye su da kuɗaɗen sata. Domin a cewar sa, wasu da dama da su ka saci kuɗaɗen gwamnati ba su jin tsadar sayen kadara, saboda kuɗaɗen ba na su ba ne. Musamman kuma su na amfani da cinikin a matsayin wurin ɓoye maƙudan kuɗaɗen da su ka sata.

“Yanzu idan ka kalli kewayen Abuja, ta kasance gasar gina danƙara-danƙan rukunin gidaje da maka-makan plaza-plaza kawai ake yi.”

Bawa ya ce kashi 90% cikin kashi 100% na kuɗaɗen gwamnati da ake sacewa, duk ana ɓoye su ne a wayau da dabarar ginawa ko sayen maka-makan rukunin gidaje da danƙara-danƙaran plaza-plaza.