Gwamnatin Zulum ta raba wa yaran makaranta Keken hawa 6000 a Barno

Domin hana dalibai zuwa makaranta latti gwamnatin jihar Barno ta raba wa daliban dake zuwa makarantun sakandare na ‘Jeka ka dawo’ kekunan hawa 6,000 a wasu kauyukan jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Abba Wakilbe ya sanar da haka ranar Laraba a taron bude makarantar koyar da fasaha da gwamnati ta gina a Wuyo dake karamar hukumar Bayo.

Wakilbe ya ce bayan haka gwamnati ta samar da kekuna 300 domin rabawa daliban da za su rika zuwa karatu a makarantar.

Bayan haka kwamishinan ya ce gwamnati ta bada takardu 231,000 domin a raba wa duk makarantun dake jihar.

Wakilbe ya ce a cikin shekara biyu gwamnatin Babagana Zulum ta gina makarantu 21 a jihar inda a ciki akwai makarantun koyar da fasaha 4.

Ya ce Zulum ya bada umurin zuba ingantattun kayan aiki da kwararrun malamai a makarantun domin samar wa dalibai ilimin boko na gari a a koda yaushe.

A jawabinsa a wurin taron shugaban karamar hukumar Bayo Mohammad Biryel ya yaba gina wannan makaranta da gwamnati ta yi ganin yadda karamar hukumar ta dade ba babu makaranta irin haka.

Biryel ya ce gina wannan makaranta zai taimaka wajen samar wa matasa ilimin boko domin zama abun moriya ga kansu da al’umma. Sannan kuma ya jinjina wa gwamnan jihar bisa ayyukan ci gaba da yake yi a jihar.