Mata ta mazinaciya ce, Miji na algungumi ne – Cacan bakin wasu ma’aurata a Kotu

A kotun gargajiya dake Igando ne wani dan sanda mai suna Rafiu Ademola mai shekara 45 ya roki kotu ta raba aurensa na shekara 4 saboda neman mazan da matarsa Rashidat take yi.

Ademola ya ce ya gano neman mazan da Rashidat ke yi a sakonin Whatsapp da take yi da maza a wayarta.

Ya ce ya kwafe wadannan sakonni na tes a wayar sa domin samun shaida akan abin da matarsa take aikatawa.

Ademola ya ce Rashidat malalaciya ce, bata girki, bata kula da ‘ya’yan su sannan bata girmama iyayensa.

Ya ce akan wadannan dalilai ya sa ya hakura da ci gaba da zama da ita, kotu ta raba auren kawai.

Ita kuwa Rashidat ta musanta duk abinda Ademola ya fadi a kotu.

Ta ce Ademola mugu ne da kulum sai ya lakada mata dukan tsiya.

Rashidat ta ce akwai ranar da Ademola ya lakada mata duka ya koreta daga gidan su zindir haihuwan uwa sannan kuma gata da tsohon ciki.

Rashidat ta ce ita ma ta gaji da auren Ademola amma tana rokon kotun da ta bata izinin rike ‘ya’yan su domin ta kula da su yadda ya kamata.

“Akwai ranar da na yi yaji daga gida bayan na dawo na iske yarana duk sun rame da wasu kuraje a jikinsu.

Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya hori ma’auratan da su koma gida su ci gaba da zama lafiya.

Koledoye ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 16 ga Disemba.