Yaƴan itatuwa 10 da mace mai ciki zata rika ci don lafiyarta da na jariri – Nazarin kwararru

Kwararrun jami’an lafiya sun yi kira ga mata masu ciki da su rika cin ‘ya’yan itatuwa domin a haifi da cikin koshin lafiya da inganta lafiyan mace mai ciki

Ga jerinsu a nan:

1. Tufa; Tufa na dauke da sinadarin Vitamin A wanda ke taimakawa wajen Kara karfin Ido sannan da sinadarin Vitamin C wanda ke taimakawa wajen warkar da rauni da kare mutum daga kamuwa da cututtuka.

Bincike ya nuna cewa yaran da uwayen su suka ci tufa a lokacin da suke dauke da cikin su basa kamuwa da ciwon Asthma da mura.

2. Ayaba; Ayaba na dauke da sinadarin Vitamin B6 wanda ke laulayin ciki da mata ke fama da shi, akwai sinadarin Fibre wanda ke taimakawa wajen saurin narkar da abinci sannan da sinadarin Vitamin C.

3. Fiya; Akai sinadarin Vitamins B, C and K, Fibre, Magnesium, Potassium, Iron, Choline da Folate Wanda ke taimakawa wajen inganta karfin kashin jariri.
Fiya na taimaka wajen gyara fata da rage kumburin kafa ga mai ciki

4. Lemun zaki: Akwai sinadarin Vitamin C, ruwa, Folate.

5. Gwaiba: Akwai folic acid, Vitamin A, B2, C da E.Gwaiba na hana mace mai ciki ta kamu da hawan jini da ciwon siga.
Sannan yana taimakawa wajen kare jini a jiki.

6. Berries; Akwai sinadarin carbohydrates wanda ke kara wa mace karfi a jiki, Vitamin C, folate wanda ke kara wa jariri karfin kashi da fiber Wanda ke taimakawa wajen narkar da abinci a ciki.

7. Gwanda; Gwanda na dauke da sinadarin lycopene wanda ke kare mace daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya tare da inganta lafiya zuciyan jariri. Akwai Kuma Vitamin A,C da E Wanda ke gyara fatar mutum.

8. Kankana; kankana na taimakawa wajen rage laulayin ciki, akwai Magnesium da Potassium wanda Watermelonke rage yawan ciwon ciki da kare mace daga bari. Akwai Kuma Vitamin A, C da a ciki.

9. Mangoro; Akwai vitamin A dake taimakawa wajen Kara karfin ido, inganta garkuwan jikin jariri daga kamuwa da cututtuka kamar su amai da gudawa.

10. Dabino; Akwai sinadarin folate da Iron wanda ke taimakawa wajen hana a haifi da mai nakasa.