Gwamnatin Kaduna ta biya Naira miliyan 205 kudin tallafin karatun dalibai ƴan asalin jihar

Hukumar ba da tallafin karatu ta jihar Kaduna, ta biya Naira miliyan 205 ga jami’o’in kasar nan a matsayin kudaden tallafa wa karatun dalibai ‘yan asalin jihar.
Shugaban hukumar Hassan Rilwan ya sanar da haka a makon jiya.
Rilwan ya ce hukumar ta biya Naira miliyan 25 ga Jami’ar Bayero dake Kano,
“Biyan wadannan kudade na daga cikin sharuddan yarjejeniyar da muka yi da jami’ar. Mun biya Naira miliyan 25 wanda tun farko burin mu shine mu biya Naira miliyan 45 domin tallafawa karatun dalibai ‘yan asalin jihar Kaduna.
“Hukumar ta kuma biya Naira miliyan 27 ga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria sannan ta biya Naira miliyan 88.63 ga jami’ar jihar Kaduna.
Bayan haka hukumar zuwa yanzu ta biya Naira miliyan 183.6 wa makarantu daban-daban a fadin Najeriya na daliban jihar Kaduna, tare da neman karin yarjejeniya da kwalejin ilimi ta Kaduna, Jami’ar Jos, ATBU Bauchi, kwalejin koyar da aikin jinya ta jihar Kaduna da sauransu.
Idan ba manta ba gwamnatin Kaduna a cikin wannan mako ta rage kudin manyan makarantu mallakar jihar. Da yawa daga cikin su an rage kusan kashi 50 cikin 100.
Wadannan makarantu sun hada da Nuhu Bamalli, kwalejin ilimi Gidan Waya, kwalejin koyar da aikin jinya ta jihar Kaduna, kwalejin koyar da kimiya da fasaha ta Shehu Idris da kwalejin koyar da kimiya da fasaha Makarfi.
Rilwan ya ce dalibai ‘yan asalin jihar Kaduna za su iya samun tallafi ta hanyar cike fom ta wannan adireshi – kdsg-scholarship.com dake yanar gizo.