Sabbin Nau’ikan Cutar Corona (EG.5 da kuma BA.2.86) Ba Abun Damuwa Bane -NCDC

Yayin da aka samu bullar wasu sabbin nau’ikan cutar corona a wasu kasashen duniya, hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya ta NCDC tace hakan bai zama abun fargaba ko barazana ba a kasar.