CCB da EFCC na binciken Muhyi Magaji, mai binciken Harƙallar Dalolin Ganduje

Hukumomin Gwamnatin Tarayya biyu, CCB da EFCC sun fara binciken Shugaban Hukumar Ƙorafe-Ƙorafen Karɓar Rashawa da Cin Hanci na Jihar Kano, Muhyi Magaji.
Kowace daga hukumomin biyu sun tura wa Hukumar KSPCAC ta Kano wasiƙar fara binciken shugaban ta Muhuyi Magaji.
Kwanan baya ne dai Magaji ya bayyana cewa ya fara binciken zargin badaƙalar cushen dalolin da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yi a lokacin da ya na kan mulkin jihar Kano.
Ganduje dai ya yi ƙoƙarin daƙile binciken na sa a lokacin da ya ke gwamna a Majalisar Dokokin Kano, sai kuma garzayawar da ya riƙa yi kotuna ya na roƙon kotu ta hana a bincike shi.
Magaji dai ya yi aiki tare da Gwamnatin Ganduje, wadda ta zarge shi da aikata ba daidai ba, kuma ta tsige shi.
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Ganduje ta yi amfani da Muhuyi Magaji ta wanda ya binciki Fadar Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi, lamarin da ya haifar da tsige shi daga sarautar Kano.
Sai dai kuma bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP a Kano ya hau mulki, ya maida Magaji kan muƙamin sa a Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Jama’a mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Kano.
Wata ɗaya bayan hawan sa, sai ya bayyana fara binciken zargin cushen dalolin Ganduje, har ya aika wa Ganduje da takardar gayyata domin ya amsa tambayoyi.
Yanzu kuma bayan Ganduje ya zama Shugaban Jam’iyyar APC, sai EFCC da CCB su ka bayyana cewa su na binciken takardun bayanan yadda Muhuyi Magaji ya riƙa kashe kuɗaɗe a lokacin da ya ke shugabancin hukumar a ƙarƙashin mulkin Ganduje.
Cikin wata wasiƙa da ta aika wa hukumar a Kano, CCB ta ce Magaji ya karya Dokar Aikin Gwamnati. Haka dai wasiƙar mai ɗauke da sa hannun S.P Gwimi, Daraktan Bincike da Leƙen Asiri ta ƙunsa.
A ranar 14 Ga Agusta, ta nemi Daraktan Ma’aikata na hukumar da Muhuyi ke shugabanci a Kano ya bayar da bayanai dangane da binciken da ake yi.
Bayanan da ake nema kuwa sun haɗa da takardar ɗaukar Muhuyi Magaji aiki, adadin albashin sa, kwafen biyan sa albashi na kowane wata daga Juli 2020 zuwa Agusta 2023.
EFCC ita kuma ta gayyaci Daraktan Kuɗaɗe na hukumar Muhuyi Magaji da ya gabatar da kan sa ga hukumar a ranar 29 Ga Agusta, domin ya je da wasu bayanai na shiga-da-fitar kuɗaɗe.
Tun a ranar 8 Ga Agusta EFCC ta rubuta wasiƙar, wadda wani jami’in ta Muktar Bello ya sa wa hannu. Ta nemi ganin kwafen hada-hadar kuɗaɗe na Magaji tun daga 2019.
Wasiƙar EFCC ta nemi iznin Magaji ya aika Daraktan Kuɗaɗe zuwa ofishin EFCC. Ta ce, “Zai zo da kwafen hada-hadar kuɗaɗen Muhuyi, sai kwafen adadin kuɗaɗen da Ofishin Akanta Janar na Jihar Kano ya bai wa Ofishin Magaji daga 2019 zuwa 2021, kuɗaɗen da Ƙananan Hukumomin Kano su ka bai wa Ofishin Magaji daga 2019 zuwa 2021, har ma kwafen kwangiloli da sunayen waɗanda aka ba kwangilolin.