Gwamnatin Buhari ta samar wa mutum miliyan 12.5 tsaftacen ruwa a Najeriya – Minista Adamu

Ministan Albarkatun Ruwa Suleiman Adamu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar wa mutum miliyan 12.5 ruwan fanfo a Najeriya.

Adamu ya fadi haka ne a taron horas da ma’aikatan hukumar ruwa da aka yi a Abuja ranar Alhamis.

Adamu ya ce samar da ruwan fanfo wa mutane da gwamnati ta yi nuni ne cewa wannan wannan gwamnati ta yi matukar maida hankali wajen samar wa mutanen kasar ababen more rayuwa a koda yaushe.

Ya ce samar da ruwan fanfo ya rataya ne a kafaddun sassan gwamnati.”Gwamnatin tarayya ta tara ruwa a cikin dam 200 dake fadin kasar nan, gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi za su samar da ruwa wa birane da kauyuka.

“A rana dam dam din dake fadin kasar nan kan saki lita 146,669,125v wa mutum miliyan 12.5 na tsawon shekara 6.

Bayan haka darekta-Janar din hukumar ruwa ta kasa NWRI farfesa Emmanuel Adanu ya yi kira ga gwamnati da ta tsaro hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ruwan fanfo mai dorewa.

Wani darekta a hukumar Martins Eduvie shima ya yi kira ga gwamnati da ta tsara hanyoyin da za su taimaka wajen ganin ruwan da ake tsatsowa daga ƙasa ya dore.