Miliyan ɗaya muka sayar da motar wanda muka kashe~ Waɗanda aka kama

Mutane biyu da ake zargin sun kashe Kyaftin Abdulkarim Bala Na’Allah, babban ɗan Sanata Bala Ibn Na’Allah, sun ce sun siyar da motar sa da suka sace akan naira N1m a jihar Katsina.

Waɗanda ake tuhuma, Bashir Muhammad, 23, da Nasiru Balarabe, 27, sun bayyana haka ne ranar da suke hira da manema labarai a hedikwatar rundunar ƴan sandan Kaduna. Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Muhammad Jalige, ya shaidawa manema labarai cewa motar ta kai darajar naira miliyan tara.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, Balarabe, mazaunin unguwar Kawo a cikin garin Kaduna, ya ce sun sayar da motar akan Naira miliyan ɗaya a Katsina.

DHA Specialist Hospital ya shirya gasar cin ƙofin ƙwallon ƙafa
Miliyan ɗaya muka sayar da motar wanda muka kashe~ Waɗanda aka kama

Balarabe ya ce ya yi amfani da kasonsa na kuɗin wajen sayen shinkafar ƴar waje, amma ma’aikatan Kwastam da ke kan iyaka kwace shinkafar.
“Na sayi buhunan shinkafa 23 da kason amma kwastam sun tare mu suka ƙwace”, in ji shi.
Wanda ake zargin, Muhammad, mazaunin hanyar Rabah a cikin garin Kaduna, ya ce bai taba sanin mamacin ba kafin faruwar lamarin.
“Wata rana, ni, Nasiru, da Usman DanKano (shi ya tsere), muna wucewa a gaban gidansa; sai muka hangi motar a cikin gidan; sai DanKano ya ce sai mun zo mun sace motar nan.
“Washegari an yi ruwan sama, don haka muka yanke shawarar zuwa gidan; lokacin da muka shiga ciki, ni da Nasiru muka buɗe wa Dankano ƙofa, wanda ke riƙe da tocila.
“Hasken fitilar ya ja hankalin mamacin, nan take ya gan mu; sai ya ɗauko wani abu daga karkashin gadonsa ya fara kokawa da Balarabe.
“A lokacin gwagwarmayar, marigayin ya faɗi sai muka yi amfani da igiya don ɗaure shi tun daga nan bai sake magana ba; sai muka ɗauki maƙullin motar muka tafi ”, inji shi Nasiru.
A halin da ake ciki, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Jalige, ya ce an sayar da motar marigayin a Jamhuriyar Nijar, amma an ƙwato ta, ya kara da cewa suna magana da ƴan sandan ƙasa da ƙasa don ganin an dawo da ita Najeriya.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 17, 2021 11:22 AM