Mutum 14 sun mutu a hatsarin mota a Kebbi, 12 ƴan gari ɗaya

Kimanin mutane 14 ne suka rasa ransu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a babbar hanyar Yauri-Koko a jihar Kebbi.

Lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis, rahotanni sun ce taho mugama ne aka yi tsakanin wasu motoci biyu ɗaya ta fito daga Sokoto zuwa yankin Kudu.

Baya ga mutum 14 da suka mutu, an samu waɗanda suka samu raunuka kuma a halin yanzu suna gadajen asibiti.

  • Mutum 14 sun mutu a hatsarin mota a Kebbi, 12 ƴan gari ɗaya
  • CAN ta kori shugabanta a Gombe bisa taya Sheikh Pantami murna

Hausa Daily Times ta samu labari cewa mutum 12 daga cikin 14 da suka mutu ƴan gari ɗaya ne daga ƙauyen Safiyel Magori na ƙaramar hukumar Gada ta jihar Sokoto kamar yadda shugaban ƙungiyar ɗaliban ƙaramar hukumar Gada, Ishaq Suleiman Alibawa ya bayyana  shafinsa na Facebook.

An yi Jana’izar su a babban asibitin Yauri a ranar Alhamis da ƙarfe 3:00 na yamma, kamar yadda wani mazaunin garin, Sani Twoeffect Youri ya bayyana.

An wallafa wannan Labari September 16, 2021 9:41 PM