Gwamna Bagudu ya taya Buhari murnar sakin ɗaliban Yawuri 31, bayan shafe watanni shida a hannun ‘yan bindiga

‘Yan bindiga sun sako ɗaliban Kwalejin Yauri su 30 da malamin su ɗaya, bayan sun shafe watanni shida a tsare.

Bayan kuɓutar su ce Gwamna Abubakar Bagudu na Jihar Kebbi ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar kuɓutar ɗaliban.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan Kebbi ya fitar, Bagudu ya bayyana cewa sakin ɗaliban wata ‘babbar nasara ce.”

Tun cikin watan Yuni aka kama ɗaliban da har yau ba a tantance yawan su ba. Kuma yaran gogarman ‘yan bindiga Dogo Giɗe ne ke tsare da su tsawon lokaci.

Kwanaki biyu bayan sace yaran dai Premium Times ta buga labarin yadda wasu daga cikin ɗaliban su ka kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane, yayin da Sojojin Najeriya su ka ƙwato su, bayan wani gumiurzu da mahara.

Mashawarcin Gwamnan Kebbi kan Yaɗa Labaran Bagudu mai suna Garba Rabi’u, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an sako wasu ɗaliban ba tare da gindiya sharuɗɗan komai ba.

Ya ce akwai sauran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga. Amma ana ci gaba da ƙoƙarin ceto su.

Sai dai kuma Rabi’u bai bayyana adadin sauran ɗaliban da har yanzu ke tsare a hannun masu garkuwar ba.

Kakakin Gwamna Bagudu, wato Yahaya Sarki, ya ce likitoci za su gwada lafiyar ɗaliban, kafin a damƙa su a hannun iyayen su.

Idan ba a manta ba, an sako wasu ɗaliban a baya, a ranar 31 Ga Oktoba, 2021, inda aka fara kai su Birnin Kebbi, kafin a damƙa kowanen su a hannun iyayen sa.

Idan an tuna, lokacin da aka kama ɗaliban ne har Gwamna Bagudu ya yi burga da cika-baki cewa zai ja zugar mafarauata su shiga dazukan Kebbi domin su ƙwato ɗaliban daga hannun ‘yan bindiga.

Har kirari Bagudu ya yi a tsakiyar mafarauta da ‘yan tauri, inda ya tuna cewa ya gaji farauta a wurin wani ƙanin mahaifiyar sa.

Sai dai duk da wannan kurari da Bagudu ya yi, ya kasa shiga dajin.