YAJIN AIKIN ADAIDAITA SAHU: Da Gaske Gwamnatin Kano Ba Ta Da Tausayi? Daga Bashir Mohammed

Duk Dan Ƙasa nagari ba zai goyi bayan mutanen da suke taka doka ba – ballantana shi da kan sa, ya taka ta yana sane. Sa’annan, duk abinda aka kawo na doka (da nufin kawo gyara a ƙasar sa) zai kasance a gaba wajen nuna farin-cikin wanzuwar wannan tsarin, sabida cigaban al’uma shine gaba da komai a wurin sa.

Batun sauye-sauye da kuma gyare-gyare da Hukumar KAROTA take kawo wa a harkar bin ƙa’idojin tuƙi a Kano, abu ne mai kyau, domin akwai wurare/fuskoki da dama wadanda aikin su ya kawo gyara…duk da akwai a bayyane, wuraren da ‘kuma’ ayyukan nasu yake kawo akasin gyaran.

Mu ƙaddara cewa, yajin aikin da Yan Adaidaita Sahu suka fara a jihar Kano, ya samo asali ne sakamakon gyara da Hukumar KAROTA take son kawo wa, shin bai dace ace mahukunta sunyi nazarin irin halin da tafiyar matuƙa KEKE NAPEP din zai jefa jama’ar gari ba?

Ko da ace masu tuƙin Adaidaita Sahu basu cika ƙa’idojin da Hukumar KAROTA, ƙarƙashin jagorancin Hon. Baffa Babba Danagundi, da kuma gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR suke buƙatar subi bane, akwai (su kan su jam’an gwamnatin), abubuwan da ya kamata su duba – domin kare haƙƙin al’uma.

Harkar sufuri, harka ce da kowa yake da ruwa da tsaki a cikin ta – domin ko baka je ba; ka aika…ko an aiko maka. Sa’annan idan wani Abu (komai ƙanƙantar sa) ya janyo aka tsayar da ita, to hatta na kwance a Asibiti; da wadanda za’a kai ta shafe su – ba ma maganar masu neman abinci ba.

Gwamnati ta nemi haraji, ko ta ƙara shi, ko ta bujiro da wata doka akan kowace irin sana’a – ba baƙon abu bane a tsarin mulki, amma abin gudu shine bujiro da dokar da ake so a dora wa wadansu tsirarun mutane, wadanda amfanin su yake shafar kowa-da-kowa a gari ta fuskoki marasa dadi.

To amma idan ya zama wajibi dokar da ake so a ƙaƙaba/sanya sai anyi amfani da ita, abu ne mai kyau (kuma wajibi) a samarwa da al’uma hanyoyin da za su rage masu radadin da dokar take haifar masu. Akwai kuskure a cikin ƙaƙaba dokar da za ta janyo a daina sufuri, kuma gwamnati bata samar da wata hanya ta daukar mutane ba.

Wannan kuwa sabida, gwamnati ana so ne ta zama mai hangen-nesa da tausayi da kuma kyautayi; ba mai ƙuntataccen tunani da ƙeta da kuma rashin kyautawa ba. Sa’annan, ina amfani gwamnati ta riƙa rikitowa kanta zagi da munanan kalamai akan ‘wataƙila’ abinda aikata shi ba dole bane – al-halin tana sane da irin halin ƙoƙari da ƙuncin-rayuwar da mutane suke ciki.

Ba bu wata mas’ala da take da hanya daya wajen warware ta – idan hagu bata yi ba; sai a gwada amfani da dama. Rashin yin haka da mutane suke zargin gwamnatin Kano tana yi, shine yake janyowa ana tunanin wadanda suke suke mulki basu iya ba; ko kuma tunanin anya gwamnati tana da ma su ba ta shawarwari kuwa. Kwanan baya, gwamnati ta bayar da sanarwar cewa za ta sayo ababen hawa domin daukar mutanen gari – shin har yanzu bata sayo bane; ko kuma ƙaddamar dasu ne ba’a yi ba?

Idan gwamnati so take yi ta rage; ko ta hana tuƙin Adaidaita Sahu din nan, ai ba wani abu ne mai wahala ba…sanarwa kawai za tayi – bayan ta samar da hanyoyin magance duk wani ƙalubale da hanin zai haifar. Amma a irin wannan lokacin daya kamata ‘alal-aƙalli’ gwamnati ya dace ta nemi yardar mutane, ba dai-dai bane ta bari al’uma su shiga halin da zai rage mata kwarjini da daraja a idanun su ba.

Yanzu a sakamakon fara yajin aikin nan, har akwai Jami’ar da dole tasa suka dage jarabawar da dalibai suke rubutawa…wanda wannan ‘kamar’ koma baya ne, da lalata tsarin karatun makarantar.

A ƙarshe, muna fata gwamnati za ta sake duba buƙatar al’uma (kamar yadda take yi kullum) wajen inganta rayuwar su, da kuma kyautata masu ta hanyoyin da suka dace.