GASAR CIN KOFIN AFRICA: Ko mikiyar Najeriya za ta iya caccake idanun ‘Fir’aunonin Masar?

Wasan da Najeriya za ta fafata da Masar a ranar 12 Ga Janairu, zai kasance mafi zafi a dukkan wasannin rukunonin kungiyoyin ƙwallon ƙafar da ke cikin gasar mai suna AFCON 2021, wadda aka fara a Kamaru.

A yayin buɗe gasa a ranar Lahadi, mai masaukin baƙi Kamaru ta doke Cote D’ivoire da ci 2:1.

Wasan Najeriya na farko za ta kara ne da Masar, inda tuni dukkan ƙungiyoyin biyu kowace ta lashi takobin cin kofin ɗungurugum.

A Rukunin D inda Najeriya ke ciki, akwai Masar, Sudan da Guinea-Bissau.

Kaftin ɗin Super Eagle Ahmed Musa ya bayyana cewa laƙanin da Najeriya za ta yi amfani da shi har ta lashe kofin, shi ne ‘yan wasa su sa kishin Najeriya a cuci, kuma su saki jiki su taka leda bakin-rai-bakin-fama, har a kai ga nasara.

A hirar da ya yi da jami’in yaɗa labarai na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, Musa ya ce ya bi ‘yan wasan Najeriya ya yi masu huɗubar kishin ƙasa.

“Na zauna da su na nuna masu cewa su saki jiki mu yi wasa saboda kishin ƙasa. Domin idan mu ka yi nasara, ƙasar mu za ta ƙara samun ɗaukaka. Iyalan mu su ma za su yi tinƙaho da mu.”

Ahmed Musa wanda ya fi kowane ɗan wasa yawan buga wa Najeriya ƙwallo a tarihi, ya ci ƙwallo ɗaya a wasan sada zumunta da Najeriya ta yi da ƙungiyar Coton Sport, a garin Garwa, inda can ne Rukunin D su ka sauka, za su yi wasannin fitowa daga rukuni.

Sun lashe wasan na sada zumunta da ci 2:0. Musa ya ce Najeriya za ta iya lashe kofin, domin ba ta tsoron ‘yan wasan kowace ƙasa a cikin dukkan waɗanda su ka fito neman lashe kofin.

Tsohon ɗan wasan Najeriya, kuma kociya Sunday Oliseh, ya bayyana cewa ƙasashe uku ne da su ka haɗa da Najeriya, Aljeriya da Tunisiya za a samu wadda za ta lashe kofin a cikin su.

Gasar AFCON 2019 dai Aljeriya ce ta lashe kofin bayan ta doke Senegal a wasan ƙarshe.

Najeriya ta zo ta biyu bayan ta doke Tunisiya a wasan neman na uku.