Fitina ta lafa, mun daƙile masu kwasar ‘ganima’ – Gwamnatin Adamawa

Gwamnatin Adamawa ta ce za ta gurfanar da sama da masu kwasar ‘ganima’ 100, bayan sassauta dokar hana walwala a Yola.
An amince a sassauta dokar hana fita dare da rana, a wata ganawa da aka yi, ranar Litinin, tsakanin gwamnati da jami’an tsaro, a Yola.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Adamawa ce, kaletapwa Farauta ta amince da sassauta dokar, a inda yanzu ta ko zama daga 6 na zuwa 6 na safe.
A ranar Litinin ce aka kafa dokar hana fita a Adamawa, yayin da talakawa su ka fara fasa kantina su na kwasar abinci
Gwamnatin Jihar Adamawa ta kafa dokar hana fita tsawon awa 24, bayan talakawa sun fara fasa rumbunan gwamnati da kantina, su na kwasar kayan abinci.
Wani ganau ba jiyau ba, ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa wadanda su ka rika fasa shagunan sun rika yin kukan matsalar abinci ta kai su ga afkawa cikin wannan mummunar matsalar da ta kai su balle kantina.
Baya ga kayan abinci, sun rika jida har da janareto, katifu da sauran kayayyaki daban-daban daga kantinan jama’a. Haka dai wani mai suna Manu Haruna ya shaida wa wakilin mu.
Kakakin Yada Labaran Gwamnan Adamawa, Humwashi Wonosikou ne ya sanar da haka a ranar Lahadin nan da rana.Ya ce ya zama tilas gwamnatin Adamawa ta kakaba dokar, domin ta magance yadda ‘yan iska ke kwasar ksyan jama’a.
Ya ce Gwamna Umaru Fintiri ya kafa dokar zaman gida dole, daga yau 30 ga Yuli, 2023. Kuma wannan doka ta na nufin ba fita waje tun daga yau, sai fa masu wani dalili na fita waje na musamman, kuma masu dauke da katin shaida.
Haka kuma Gwamna Fintiri ya roki a kai zuciya nesa, a daina kwasar kayan jama’a, a bi doka da oda.Ya kuma gargadi duk wanda bai ji bari ba, to zai ji hoho.
Ita ma Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa, ta gargadi jama’a cewa duk wanda ya karya doka, to ya kuka da kan sa.
Kakakin Yada Labaran su Afolabi Babatola, ya ce an baza zaratan jami’an tsaro da za su tabbatar da cewa kowa ya kiyaye umarnin zaman gida tilas da gwamnatin jihar ta kakaba.