Najeriya Ta Kai Zagayen ‘Yan Sha-Shida A Gasar Cin Kofin Duniya
Kungiyar Super Falcons wacce ita ce ta 40 a iya taka leda a fagen wasan kwallon kafa na mata a duniya, ba ta sha kaye ko daya ba a wasannin da ta buga, yanzu kuma ta doshi zagayen kwaf-daya.