BABBAN RASHI A KOTUN KOLI: Chima Nweze, alkalin da ya jagoranci kwace takarar Machina aka bai wa bAhmad Lawan, ya rasu 

Majiya daga Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da rasuwar Babban Mai Shari’a Centus Chima Nweze, wanda ya rasu ya na da shekaru 64 a duniya.
Har zuwa yanzu dai ba a ji musabbabin rasuwar ta sa ba, domin Kotun Koli ba ta kai ga yin wata sanarwa ba.Nweze ya rasu shekaru shida kafin lokacin yin ritayar sa daga aiki.
Kafin rasuwar sa, shi ne Babban Mai Shari’a mai daraja ya biyar a Kotun Kolin Najeriya.
Nweze zama Mai Sharia na Kotun Koli cikin 20214. Kafin rasuwar sa su 13 ne a Kotun Koli.
Ya fara zama alkalin Babbar Kotun Jihar Enugu a cikin Nuwamba, 1995. Amma kuma ya zama Babbabn Mai Sharia a Kotun Koli, cikin Oktoba, 2014.
Shi ne Mai Shari’ar da ya jagoranci wasu alkalan K0tun Koli, suka tabbatar wa Sanata Ahmad Lawan takara, yayin da suka jaddada halascin kwace takkarar daga Machina, wanda APC ta zaba.