‘Mun sha ruwan wuta ba ƙaƙƙautawa’ -Mataimakin Gwamnan Kebbi, bayan ya sha da kyar

Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Samaila Yombe, ya bayyana yadda mahara su ka riƙa yi wa tawagar sa ruwan wuta, a lokacin da ya ke rangadi da zagayen ƙara wa sojojin Najeriya ƙwarin guiwar yaƙi da ‘yan bindiga.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda Yombe, wanda tsohon soja ne ya faɗa tarkon ‘yan ta’adda, waɗanda suka buɗe masu wuta a kusa da Kanya, cikin Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi.

A cikin rahoton an bada bayanin yadda ‘yan bindigar su ka bindige sojojin Najeriya 13.

Harin da mahara su ka kai wa Yombe ya zo ne kwanaki biyu bayan mahara sun bindige ‘yan sa-kai 63 cikin Ƙaramar Hukumar Sakaba a dai Jihar Neja ɗin.

‘Yadda Mahara Suka Buɗe Mana Wuta, Aka Yi Mummunan Gumurzu’ -Mataimakin Gwamnan Kebbi:

Da ya ke wa manema labarai jawabi a Birnin Kebbi a ranar Talata, Yombe ya ce abin da ya faru da su, wani ƙazamin yaƙi ne ya ritsa da su.

“Wani ƙazamin yaƙi ya ritsa da mu jiya a Kanya. Abin da ya faru shi ne, ‘yan bindiga sun saje da mutanen cikin ƙauyen Kanya, ta yadda da wahala a ce jami’an tsaro su iya far masu a lokacin. Saboda idan aka yi haka, Allah kaɗai ya san asarar fararen hular da za a yi a wurin.

“Saboda haka sai na cewa Kwamandan Sojoji wanda ke tare da mu cewa mu gaggauta ficewa daga cikin garin. Dabarar yin haka ita ce, idan muka fita, ‘yan bindigar bin mu za su yi. To idan aka kafsa a daji kuwa ba za a yi asarar rayukan fararen hula ba.

“To irin wannan yaƙi ka san tilas a kowane ɓangare a samu asarar rayuka. Amma dai an fi kashe ‘yan bindiga, duk da cikin sojojin ma an kashe, amma dai ba su kai yawan ‘yan bindigar da aka kashe ba.” Cewar sa.

Yombe ya jinjina wa Sojojin Barikin Zuru a kan bijintar fatattakar mahara da su yi.

Ya ce an rasa rayukan sojoji ne saboda maharan sun saje a cikin jama’a, amma duk da haka, an fi kashe ‘yan bindiga ɗin.

“Kun san su ‘yan bindiga ba su barin gawar ‘yan uwan su. Idan ma ta kama su bar su ɗin, to ƙonewa su ke yi. Saboda na ga lokacin da wani ɗan bindiga ya je ya tultula fetur a kan gawar wan ɗan’uwan su, ya cimma mats wuta.

“Kuma bayan da sojoji su ka ɗauke gawarwakin wasu mahara biyu, na ga lokacin da suka ɗauke gawarwakin na ‘yan’uwan su.” Inji shi.

“Yawan ‘yan bindigar da suka buɗe mana wuta za su kai 140 zuwa 200. Alhali mu kuma muna tare da sojoji 32 kaɗai.

“Sojojin nan sun yi ƙoƙari sosai, saboda su fa rakiyar Kwamandan Zuru su ka je, wanda ke tare a cikin tawagar rakiya ta.”

Ya ce dukkanin ‘yan bindigar su na ɗauke da AK-47 ne.