Abdulrasheed Bawa ya farfado kuma yana nan cikin koshin lafiya – Hukumar EFCC

Kakakin hukumar EFCC ya Wilson Uwujaren ya bayyana cewa shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa da ya yanke jiki ya fadi a wajen taro a fadar shugaban kasa ya farfado kuma yana cikin koshin lafiya.

Uwajaren yace nan ba da dadewa ba za dawo ya ci gaba da aikin sa.

A ranar Alhamis ne shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasa a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron ranar Sanin kai wato National Identity Day.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Bawa dai ya fara jawabin sa kenan bai dade ba sai kawai ya fara rufe fuska da hannu yan cewa ayi hakuri ba zan iya magana ba, a zo a taimake ni, daga nan ne ministan sadarwa ya rike shi zuwa wurin zama. Sai dai kuma ko da ya zauna sai ya kasa zama ya yanke jiki ya fadi.

Daga nan sai aka taimaka masa aka fita dashi daga dakin taron.