Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulƙadir ya rasu

Rahotanni da muke samu daga masarautar Gaya da ke jihar Kano sun tabbatar da rasuwan Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulƙadir.

Masarautar Gaya na ɗaya daga cikin sabbin masarautu masu jar sanda (First Class Emirate) da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ƙirƙiro a shekaru uku baya.

Ƙarin bayani na tafe.

An wallafa wannan Labari September 22, 2021 11:32 AM